Koma ka ga abin da ke ciki

YULI 24, 2017
RASHA

Kotun Oryol Ta Ce A Ci gaba da Tsare Malam Dennis Christensen

Kotun Oryol Ta Ce A Ci gaba da Tsare Malam Dennis Christensen

A ranar 20 ga Yuli, 2017, kotun yankin Sovietskiy da ke birnin Oryol, ya ce a ci gaba da tsare Dennis Christensen har sai 23 ga Nuwamba na 2017. Mallam Christensen asalin ɗan ƙabilar Danish ne kuma shi Mashaidin Jehobah ne. A ranar 25 ga Mayu ne aka kama shi sa’ad da Hukumomin Tsaron ƙasar Rasha suka je inda Shaidun Jehobah suke ibadarsu a garin Oryol ba gaira ba dalili.

Lauyoyinsa sun nemi a ba da belin sa kuma sun shirya su biya kudin belin. Amma kotun ya ki a yi belin sa duk da cewa ba a taba samun sa da laifi ba kuma ba a taba zargin sa da yin fada ba.

An ci gaba da tsare mallam Christensen ne bayan da Kotun Koli na kasar Rasha ya dakatar da ayyukan ibada na Shaidun Jehobah a duk fadin kasar. Bayan shekaru da yawa da hukumomin kasar Rasha suka yi suna kokarin tsananta wa Shaidun Jehobah a kasar da kuma ayana su a matsayin masu “tsattsaurar ra’ayi,” yanzu sun yi nasarar sanya ayyukan ibada na Shaidun Jehobah a matsayin ayyukan da suka saba wa dokar kasar.

Kate M. Byrnes, wanda Jami’ar Diflomasiyar kasar Amirka ce a Turai, wato U.S. Mission to the Organization for Security and Cooperation in Europe, ta tofa albarkacin bakinta game da yadda ake tsananta wa Shaidun Jehobah a kasar Rasha: “Muna sane da hukuncin da Kotun Kolin Rasha ya yanke a ranar 17 ga Yuli, 2017 na dakatar da ayyukan ibada na Shaidun Jehobah a kasar baki daya da kuma kwace Ofisoshinsu har da wuraren ibadarsu guda 395, domin zargin da ake musu cewa su masu ‘tsattsaurar ra’ayin addini’ ne.

Abin takaici ne cewa, Shaidun Jehobah sama da 175,000 a kasar Rasha za su fuskanci hukunci idan suka yi ayyukan ibadarsu. Mun damu da yadda ake kafa dokoki a kan ‘tsattsaucin ra’ayi’ don a take hakkin mutanen kirki da ba su da yawa da suke yin addininsu cikin salama a kasar Rasha.”