Koma ka ga abin da ke ciki

Yuli 27, 2017
RASHA

Hukumar Rasha Ta Ce Littafi Mai Tsarki Bai Dace Ba

Hukumar Rasha Ta Ce Littafi Mai Tsarki Bai Dace Ba

Sabon Bayani: Kotun da ke Birnin Vyborg ta dakatar da ƙai 9 ga watan Agusta, 2017.

A ranar 28 ga Yuli, 2017, Kotun Vyborg zai sake saurarar karar da aka shigar da ke neman kotun ya sanar cewa juyin Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures wanda Shaidun Jehobah suka wallafa a yaren Rasha, bai dace ba. Tun a watan Afrilu, 2016 ne Kotun ya daga karar nan domin wani lauya mai suna Leningrad-Finlyandskiy ya roki kotu da ya ba shi dama don ya nemi kwararru da za su bincika juyin New World Translation don su tabbatar cewa bai dace.

Bayan wasu watanni ne aka kammala binciken da aka yi kuma aka ba wa kotun takardar binciken a ranar 22 ga Yuni, 2017. Wadanda suka yi nazarin sun yarda da da’awar da ake yi cewa wannan Littafi Mai Tsarki littafi ne da ke bayyana “tsattsauran ra’ayi.” Shaidun Jehobah ba su yi mamaki ba don sun san cewa abin da manazartan za su fada ke nan. A binciken da suka yi, sun yi da’awar cewa New World Translation ba “Littafi Mai Tsarki ba ne.” Amma sun fada hakan ne domin ba sa so su keta dokar da ta haramta bayyana littattafan addini irin su Littafi Mai Tsarki cewa ba su dace ba. Kari ga haka, sun yi binciken bisa koyarwar makarantun Fastoci ne, wato theology. Sun ce Shaidun Jehobah sun yi amfani da harufa hudu * na Ibrananci da ke nufin Jehobah a cikin New World Translation don ya jitu da koyarwarsu.

^ sakin layi na 3 Harufa hudun nan (יהוה), wato YHWH ko kuma JHVH sunan Allah ne da Ibrananci kuma ya bayyana kusan sau 7,000 a Nassosin Ibrananci