Koma ka ga abin da ke ciki

28 GA YUNI, 2016
RASHA

Ana Jira A Ji Abin da Kotu Za Ta Ce Game da Barazanar Rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha

Ana Jira A Ji Abin da Kotu Za Ta Ce Game da Barazanar Rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha

Nan ba da dadewa ba, Kotun Gunduma na birnin Tver za ta yanke shari’a a kan wata karar da Shaidun Jehobah suka shigar a kasar Rasha, domin ana barazanar rufe ofishinsu na kasar. Mai Shigar da Kara a Madadin Gwamnatin Rasha ya aika wa Shaidun Jehobah wasikar gargadi cewa za ta rufe ofishinsu na kasar Rasha domin tana zargin Shaidun Jehobah da aikata “ayyukan tsattsauran ra’ayi.”

Shaidun Jehobah sun bukaci kotun ta bayyana cewa wannan gargadin ba bisa ka’ida take ba. Wannan gargadin yana muzguna ‘yancin da Shaidun Jehobah suke da shi na gudanar da addininsu, kuma an shirya shi ne domin a yi amfani da dokar yaki da tsattsauran ra’ayi a hanyar da ba ta dace ba.

Wakilin ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar Rasha mai suna Vasiliy Kalin, ya ce: “Ba mu taba saka hannu a ayyukan tsattsauran ra’ayi ba, “ kuma ya kara da cewa “Muna fatan za a daidaita wannan rashin adalcin da ake mana.”