Kotun Gunduma ta Tver da ke Moscow ta amince ta saurari karar da Shaidun Jehobah suka daukaka game da barazanar da Mai Shigar da Kara a Madadin Gwamnati ya yi na kokarin rufe ofishinsu da ke kasar. Kotun za ta saurari karar a ranar 18 ga Yuli, 2016 don ta ga ko barazanar tana bisa ka’ida.

’Yan majalisa da ke birnin Arkhangelsk su ma sun kai karar Shaidun Jehobah a wurin Ministan Shari’a mai suna Aleksandr Konovalov. A karar da suka shigar, sun bukaci gwamnati ta kafa doka da za ta sa a rufe ofishin Shaidun Jehobah da kuma hana su gudanar da ayyukansu na ibada a kasar gaba daya.