Koma ka ga abin da ke ciki

27 GA SATUMBA, 2016
RASHA

An Sake Dage Sauraron Karar a kan Barazanar Rufe Hedkwatar Shaidun Jehobah a Kasar Rasha

An Sake Dage Sauraron Karar a kan Barazanar Rufe Hedkwatar Shaidun Jehobah a Kasar Rasha

A ranar 23 ga watan Satumba 2016, Kotun Gunduma na birnin Tver da ke kasar Rasha ta dage zamanta na sauraran karar da Shaidun Jehobah suka shigar a kan barazanar da hukumomi suke yi na rufe hedkwatar Shaidun Jehobah a kasar Rasha. Kwana uku kafin kotun ta saurari karar, wanda ya shigar da karar Shaidun Jehobah ya kai karin bayani a cikin takardar da ke dauke da shafuffuka fiye da 200. Shaidun Jehobah sun bukaci a ba su lokaci don su yi nazarin sababbin hujjojin da aka shigar kuma alkalin ya zabi ranar 12 ga Oktoba 2016, don kotun ta sake zama. A wannan ranar ne kotun za ta saurari karar da Shaidun Jehobah suka daukaka kuma ta tantance ko barazanar rufe hedkwatarsu a kasar tana bisa doka.