Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA OKTOBA, 2013
KOREA TA KUDU

Duniya Ta Yi Tir da Rashin Adalci na Koriya ta Kudu

Duniya Ta Yi Tir da Rashin Adalci na Koriya ta Kudu

Kasar Koriya ta Kudu tana daure darurruwan matasa da ba su aikata laifin kome ba a kurkuku. Me ya sa? Matasan nan Shaidun Jehobah ne da suka yanke shawarar yin rayuwa da ta jitu da lamirinsu, kuma abin da ya hana su shiga soja ke nan. Kasar Koriya ba ta da wata doka da take kāre wadanda suka ki shiga soja, saboda haka, dukan Shaidun da ake tuhumar su a kan wannan batun ana tura su kurkuku. A cikin shekaru 60 da suka gabata, an tsare Shaidun Jehobah fiye da 17,000 a kurkuku domin sun ki shiga soja saboda imaninsu.

Domin a jawo hankalin mutane ga abin da ke faruwa, babban ofishin Shaidun Jehobah a kasar Koriya ta Kudu ta buga wata kasida mai jigo  Conscientious Objection to Military Service in Korea (Kin Shiga Soja a Kasar Koriya Saboda Imani). Kasidar ta bayyana yadda kasar Koriya ta ki bin ka’idodi da kasashen duniya suka kafa don kāre wadanda suka ki shiga soja saboda imaninsu. Ta kuma ba da labarin Shaidun Jehobah matasa maza da aka kai su kurkuku domin sun kudura cewa ba za su saba wa imaninsu ba. Wani mai suna Dae-il Hong, da yake wakiltar ofishin Shaidun Jehobah a kasar Koriya da Philip Brumley, wanda yake wakiltar Shaidun Jehobah a jihar New York sun ba da karin haske a kan wannan rashin adalci da ya dade yana aukuwa.

Wane mataki ne kasashen duniya suka dauka game da rashin adalci da ke aukuwa a kasar Koriya ta Kudu?

Philip Brumley: Wasu kasashe sun riga sun yi tir da yadda kasar Koriya ta ki amincewa da ’yancin da kowa yake da shi ya ki yin abin da ya saba wa imaninsa. A wani taron Majalisar Dinkin Duniya ta Universal Periodic Review na kwanan nan, kasashe takwas, wato, Faransa, Jamus, Sifen, Amirka, Ostareliya, Poland, Slovakia, da Hungary, duk sun gargadi kasar Koriya ta daina hukunta mutane idan suka ki shiga soja domin imaninsu kuma su ba su damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja. *

Dae-il Hong: A kararaki guda 4 da suka shafi mutane 501 da suka ki shiga soja saboda imaninsu, Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya don Kāre Hakkin Dan Adam, wato, UN Human Rights Committee (CCPR) ya yanke shari’a da ta nuna cewa Lardin Koriya ya keta hakkin dan Adam sa’ad da ya yanke wa Shaidun Jehobah hukunci har da daure su a kan wannan batun. Kwamitin ya nuna cewa “’yancin ki da aikin soja domin ya saba wa imanin mutum ya jitu da ’yancin tunani da lamiri da addini. Saboda wannan ’yancin, kowa yana da izinin ki da aikin soja idan yin hakan zai saba wa imaninsa. Kuma kada a yi amfani da karfin soja wajen tilasta wa mutane su yi wannan aikin.” *

Hakazalika, wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta Karē Hakkin ’Yan Adam, wato, Human Rights Council, ta jawo hankalin mutane ga wannan batun sa’ad da ta kaddamar da wani rahoto mai jigo: “Analytical report on conscientious objection to military service.” Wannan rahoton ya bayyana ka’idodin shari’a da kasashen duniya suka kafa, wadanda suka nuna cewa kowane mutum yana da ’yancin ki da wani aiki bisa ga imaninsa kuma ya hana tilasta wa mutane su yi wannan aikin ko ta wajen kai su gaban shari’a sau da sau ko kuma ta wajen hukunta su. *

Mene ne gwamnatin Koriya ta yi game da matsayin da kasashen duniya suka dauka a kan wannan batun?

Ginin Kotun Koli

Philip Brumley: Gwamnatin Koriya ta ki amince da shari’ar da CCPR ta yanke a kan wannan batun. Da hakan, kasar Koriya ta ki bin sharudan yarjejeniyar da ta yi da kasashen duniya kuma ta ki amince da ’yancin ’yan Adam na ki da aikin da ya saba wa imaninsu. Kari ga haka, Kotun Koli da Kotun Tsara Dokar Kasa ta kasar Koriya sun yi banza da wannan shari’ar da CCPR ta yanke sa’ad da suka yi watsi da karar da Shaidun nan suka daukaka saboda imaninsu. Majalisar Wakilai ta kasar Koriya ta ki ta tsara aikin farar hula da ba za ta saba wa imanin Shaidun nan a maimakon aikin soja ba, kuma ba ta kafa wata doka don kāre su ba.

Ta yaya daurin nan ya shafi galibin matasa Shaidun Jehobah?

Dae-il Hong: Wadannan matasan mazaje ne masu karfin hali. Ba sa gudu sa’ad da gwamnati ta kira su su zo su shiga aikin soja, ko da yake sun san cewa za a hukunta su kuma a kai su kurkuku a karkashin tsarin da ake da shi a kasar yanzu. Kafin a tsare su, su ’yan kasa ne da suka cancanci a yi koyi da su, kuma bayan sun shiga kurkuku, suna zama fursunoni da suka cancanci a yi koyi da su. Amma, abin bakin ciki shi ne bayan an sake su, ana bata musu suna cewa su masu laifi ne kuma hakan yana sa ya yi wuya su sami aiki da ma’aikatan gwamnati ko kuma manyan kamfanoni masu rajista. An hana su jin dadin rayuwa na tsawon shekara daya da rabi a lokacin da suke kurkuku, kuma iyalansu sun yi kewarsu sosai. Irin wahalar da suke sha ba ta dace ba.

Shin daure Shaidun Jehobah da ake yi a kasar Koriya kamar dai su masu aikata laifi ne domin kawai sun ki shiga soja ya dace ne?

Dae-il Hong: Hakika, hakan bai dace ba! Wadannan matasa ba masu aikata laifi ba ne. An san Shaidun Jehobah a kasar Koriya da kuma fadin duniya a matsayin masu bin doka da son zaman lafiya kuma suna marmarin taimaka wa mutane a yankinsu. Suna ladabta masu mulki, suna bin doka, suna biyan haraji kuma suna bin duk wani tsarin da gwamnati ta kafa don amfanin jama’a. Alal misali, a kwanan nan, wata alkalin kotun wani gunduma a kasar Koriya ta yanke ma wani matashi Mashaidin Jehobah hukuncin dauri domin ya ki shiga soja, saboda hakan ya saba wa imaninsa. Bayan alkalin ta ce ba ta da wani zabi fiye da ta bi hukuncin da kotun ya yanke cewa dan’uwanmu yana da laifi, sai ta karanta hukuncin ga jama’a. Farat daya, sai alkalin ta rufe fuskarta da takardun da take rike da su kuma ta fashe da kuka. Hakika rashin adalci da aka yi sa’ad da aka yanke wa matashin nan hukuncin da ya mai da shi tamkar mai aikata laifi ya sa ta bakin ciki sosai har ta rikice na dan lokaci. Wasu masu sauraron wannan hukunci sun lura da wannan rashin adalci kuma hakan ya sa su ma suka zub da hawaye.

Philip Brumley: Hakika, yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin Koriya ta warware wannan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa kuma ta kafa tsarin da zai daukaka ’yancin da kowane dan Adam yake da shi na ki da aikin da zai saba wa imaninsu.

^ sakin layi na 5 Rahoton Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta Karē Hakkin ’Yan Adam na “Report of the Working Group on the Universal Periodic Review,” ranar 12 ga Disamba 2012, A/HRC/22/10, shafuffuka na 7 da 22, sakin layi na 44 da 124.53.

^ sakin layi na 6 Jong-nam Kim et al. v. The Republic of Korea, communication no. 1786/2008, Ra’ayoyin da Kwamitin ya daukaka a ranar 25 ga Oktoba 2012, shafi na 7, sakin layi na 7.4

^ sakin layi na 7 Rahoto daga Hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Kan Karē Hakkin ’Yan Adam, na “Analytical report on conscientious objection to military service,” na ranar 3 ga Yuni 2013, A/HRC/23/22, shafuffuka na 3-8, sakin layi na 6-24; shafuffuka na 9 da 10, sakin layi na 32 da 33.