Koma ka ga abin da ke ciki

KAZAKISTAN

An Jefa Su a Kurkuku Domin Imaninsu

An Jefa Su a Kurkuku Domin Imaninsu

A ranar 2 ga Mayu, 2017, Alkali Talgat Syrlybayev ya yanke wa Teymur Akhmedov hukuncin shekara biyar a kurkuku domin ana zarginsa da “jawo kiyayya domin addini” da kuma “daukaka mazaunan kasar fiye da wasu domin addininsu.” Alkalin ya kuma hana Malam Akhmedov yin duk wasu “ayyukan ibadarsa” na shekara uku. Kari ga haka, a ranar 20 ga Yuni kotun da ke birnin Astana ta ki saurarar daukaka kara da Malam Akhmedov ya yi, duk da cewa akwai abubuwan da suka nuna bai da laifi.

An Zarge Shi da Taka Doka Ba Tare da Hujja Ba

Zargin da ake wa Malam Akhmedov ya soma ne sa’ad da yake tattaunawa da wasu “Dalibansa na Littafi Mai Tsarkin” da suke da’awar cewa suna son su san imanin Shaidun Jehobah a shekara ta 2016. A tattaunawar da ya yi da su cikin wata 7, yana amfani da Littafi Mai Tsarki don ya tabbatar masu da abin da ya yi imani da shi. Amma abin da Malam Akhmedov bai sani ba shi ne, ashe suna daukan maganarsa bisa tef a boye a duk tattaunawar da yake yi da su don su sami hujjar nuna cewa ya saba abin da ke Talifi na 174 sashe na 2 na dokar kasar Kazakhstan. Dokar ta hana “jawo . . . kiyayya domin addini” da kuma “daukaka mazaunan kasar fiye da wasu domin addininsu.” Domin hakan zai kai ga “sukar . . . ra’ayin wasu ‘yan kasar don irin addinin da suke bi” da kuma “daraja wasu fiye da wasu don addininsu.”

Duk da haka, Malam Akhmedov ya ƙi da zargin da ake masa cewa ya tāka dokar ƙasar. Amma ya ce yana bayyana abin da ya yi imani da shi ne don yana da ’yancin yin hakan bisa Talifi na 18 da 19 na dokar International Covenant on Civil and Political Rights (ICCPR). Dokar ta ba wa kowa “’yancin bin addini da lamirinsa yake so” da kuma “fadin ra’ayinsa.”

Kwamitin UN da ke kāre hakkin ‘yan Adam, wanda kuma ita ce ke lura don kada a tāka dokar ICCPR ta mai da hankali sosai ga kasar Kazakhstan. Kwamitin ta lura da yadda kasar take “amfani da Talifi na 174 na ICCPR a hanyar da ba ta dace ba” wajen cin zarafin mutanen da suke amfani da ’yancinsu na bin addinin da suke so. A wani rahoton da kwamitin ya fitar a ranar 9 ga watan Agusta, 2016, ya umurci kasar Kazakhstan ta bai wa duk wani dan kasar ‘yancin bin addini da kuma imani har ma da yin ayyukan addininsa. Kwamitin ya kuma ce kasar ta yi wa talifi na 22 na dokar kasar gyarar fuska don ta jitu da ICCPR, bayan haka, ta kuma yi wa duk wata doka ta kasar da ta hana ’yancin bin addini gyara bisa talifi na 18 na dokar ICCPR.

Da yake magana game da yadda kasar Kazakhstan take “amfani da talifi na 174 na ICCPR a hanyar da ba ta dace ba,” Malam Heiner Bielefeldt, wanda a dā shi ne mai ba da rahoto ga UN a kan ‘yancin bin addini da kuma imani, ya fitar da rahoto a 2014 kuma ya ce Kazakhstan ta “canja yadda take bayyana abin da tsattsaurar ra’ayin addini yake nufi kuma ta maye gurbinta da “bayyani mai sauki.” Idan ba haka ba, dokar za ta rika tāka “’yancin addini da kuma imanin wasu.”

An Saka Teymur Akhmedov a Kurkuku Duk da Cewa Ba Shi Da Laifi

A ranar 20 ga watan Janairu, 2017 Kotun na 2 da ke yankin Saryarka, a Astana ta tura Mallam Akhmedov jiran shari’a a kurkuku. Hukumomin fursunan sun yi masa dka don su tilasta masa ya amince da cewa ya yi laifi duk da cewa Mallam Akhmedov wanda yake da shekara 61, yana bukatar jinyar gaggawa domin yana fama da wani kumburi da ke fid da jini. Lauyoyinsa sun daukaka kara zuwa wani Rukunin da ke ba da rahoto ga UN a kan ‘yancin addini da imani da kuma ’yancin yin taro da tarayya cikin lumana. Bayan kotu da ke birnin Astana ta ki saurarar daukaka kara da ya yi a ranar 20 ga Yuni, 2017. Lauyoyin Mallam Akhmedov suna kokarin kara daukaka karar.

A ranar 2 ga Oktoba, 2017, Kungiyar Gudanarwa game da Tsare-tsare wato WGAD, ta bayyana cewa bai dace gwamnati Kazakhstan ta saka Mallam Akhmedov a kurkuku ba, kuma ta ba da umurni a sake shi ba tare da bata lokaci ba. Kugiyar ta lura cewa Mallam Akhmedov yana gaya wa wasu abin da ya yi imani da shi ne, “a cikin kwanciyar hakanli, kuma bai taka doka ba,” sun lura cewa an saka shi a kurkuku ne don an ki jinin Shaidun Jehobah. Kwana daya bayan Kugiyar ta gaya wa jama’a shawarar da ta yanke, lauyoyin Mallam Akhmedov sun daukaka kara zuwa Kotun Kolin kasar Kazakhstan don a bin umurnin da WGAD ta ba da, a saki Mallam Akhmedov daga kurkuku ba tare da bata lokaci ba, kuma a wanke sunansa. Yanzu suna jira cewa gwamnatin Kazakhstan za ta saki Mallam Akhmedov daga kurkuku ba da dadewa ba.

Abubuwan da Suka Faru

 1. 2 ga Oktoba, 2017

  Kungiyar WGAD ta bayyana cewa an saka Teymur Akhmedov a kurkuku ba tare da ya yi laifi ba kuma a sake shi ba tare da bata lokaci ba.

 2. 20 ga Yuni, 2017

  Kotun Astana ta ki saurarar daukaka kara.

 3. 2 ga Mayu, 2017

  An yanke masa hukuncin zama na shekara 5 a kurkuku.

 4. 13 ga Maris, 2017

  An shigar da kara kotu.

 5. 1 ga Maris, 2017

  An ki a amince da yadda ya so ya wanke sunansa.

 6. 20 ga Fabrairu, 2017

  Ya shigar da kara yana neman a wanke shi daga zargin da ake masa na tāka dokar ƙasa.

 7. 30 ga Janairu, 2017

  Kotun da ke Astana ya yi watsi da daukaka kara da aka yi.

 8. 18 ga Janairu, 2017

  An kama Malam Teymur Akhmedov kuma an jefa shi a kurkuku na wata biyu don jiran shari’a.