Kasar Eritiriya tana tsare Shaidun Jehobah a kurkuku tare da ’yan kananan addinai ba tare da an yi musu shari’a ko kuma an tuhume su da wani laifi ba. Ana tsare Shaidun Jehobah maza da mata har da yara da tsofaffi saboda ayyukan ibada ko kuma wasu dalilai da ba a ambata ba. Ana tsare matasa maza a kurkuku domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu.

Sa’ad da kasar Eritiriya ta sami ’yancin kanta a shekara ta 1993, Shaidun Jehobah sun rasa nasu ’yancin a kasar. Shugaban kasar Afewerki ya janye shaidar Shaidun Jehobah na zama ’yan kasa a cikin sanarwar da ya yi a ranar 25 ga Oktoba, 1994, domin ba su sa hannu a zaben samun ’yancin kai na kasar a shekara ta 1993 ba kuma sun ki su shiga soja domin imaninsu. Tun daga lokacin, hukumomin tsaro a kasar Eritiriya sun tsare Shaidun Jehobah a kurkuku, sun gana musu azaba kuma sun tsananta musu don su musanta imaninsu.

Hukuncin Zama a Kurkuku Babu Iyaka a Cikin Yanayi Mai Wuya

A ranar 24 ga Satumba, 1994, an tsare maza uku wato, Paulos Eyassu da Isaac Mogos da Negede Teklemariam, a kurkuku domin sun ki shiga soja saboda imaninsu kuma har wa yau suna tsare a kurkuku. An tsare wasu Shaidun Jehobah a cikin babban akwatin karfe, wasu kuma a cikin gidan dutse ko na karfe da rabinsa na karkashin kasa. A watan Yuli, 2011, wani da aka tsare a Meitir Prison Camp mai suna Misghina Gebretinsae ya rasu shekararsa 62, domin tsananin zafi sa’ad da ake gana masa azaba a wani wuri da ake kira “karkashin kasa.” Yohannes Haile ma ya rasu yana da shekaru 68 a ranar 16 ga Agusta, 2012, domin irin wannan azabar, bayan ya yi kusan shekara hudu a kurkukun Meitir Camp. An saki wasu Shaidun Jehobah daga Meitir Camp bayan sun yi rashin lafiya mai tsanani.

Wadanda Aka Kama a Kwanan Nan

A ranar 14 ga Afrilu, 2014, yayin da Shaidun Jehobah a fadin duniya suke tunawa da mutuwar Yesu Kristi, hukumomin Eritiriya sun kama Shaidun Jehobah fiye da 90. Wadanda aka kama sun hada da maza da mata daga ’yan shekara daya da wata hudu zuwa mai shekara 85. A ranar 27 ga Afrilu, 2014, hukumomin Eritiriya sun kama Shaidun Jehobah 31 sa’ad da suke yin taron ibada. Ba a ba da karin bayani game da dalilin da ya sa aka tsare su da kuma irin yanayin da suke ci ba.

Jerin Shekaru

 1. 23 ga Janairu, 2015

  Shaidun Jehobah guda 58 ne aka tsare a kurkuku ba tare da an yi musu shari’a ko kuma an tuhume su da wani laifi ba.

 2. 12 ga Disamba, 2014

  Shaidun Jehobah guda 64 ne aka tsare a kurkuku ba tare da an yi musu shari’a ko kuma an tuhume su da wani laifi ba.

 3. 25 ga Yuli, 2014

  An saki yawancin wadanda aka kama a ranar 14 ga Afrilu, amma guda 20 a cikin wadanda aka kama a ranar 27 ga Afrilu suna nan a tsare har wa yau; Shaidun Jehobah guda 73 ke nan suke tsare a kurkuku.

 4. 27 ga Afrilu, 2014

  An kama Shaidun Jehobah guda 31 sa’ad da suke yin taron ibada.

 5. 14 ga Afrilu, 2014

  An kama Shaidun Jehobah fiye da 90 sa’ad da suke yin taron Tuna da Mutuwar Kristi.

 6. Nuwamba, 2013

  Adadin Shaidun Jehobah guda 52 ne aka tsare a kurkuku a cikin yanayi mai wuya.

 7. 16 ga Agusta, 2012

  Yohannes Haile, ya rasu a kurkuku a cikin yanayi mai wuya sa’ad da yake da shekaru 68.

 8. Yuli 2011

  Misghina Gebretinsae, ya rasu a kurkuku a cikin yanayi mai wuya sa’ad da yake da shekaru 62.

 9. 28 ga Yuni, 2009

  Hukumomin Eritiriya sun kai hari a wani gidan Mashaidin Jehobah yayin da ake yin taron ibada kuma sun kama duka Shaidu 23 da suka halarci taron, daga mai shekara 2 zuwa 80. Adadin Shaidun Jehobah da suke tsare a kurkuku ya haura zuwa 69.

 10. 28 ga Afrilu, 2009

  Hukumomin Eritiriya sun kwashi duka Shaidun Jehobah da aka tsare a ofishin ’yan sanda zuwa kurkukun Meitir Prison Camp. Mutum guda ne kawai suka bari a ofishin ’yan sandan.

 11. 8 ga Yuli, 2008

  Hukumomin Eritiriya sun kai hari a wasu gidaje da wuraren aiki don su kama Shaidun Jehobah guda 24, kuma yawancin wadanda suka kama su ne masu yi wa iyalansu tanadin abinci.

 12. Mayu 2002

  Gwamnati ta haramta duka addinai da ba sa karkashin addinai hudu da gwamnati ta amince da su.

 13. 25 ga Oktoba, 1994

  Shugaban kasa ya ba da dokar da ta janye shaidar Shaidun Jehobah na zama ’yan kasa kuma ta kwace duka hakkinsu.

 14. 24 ga Satumba, 1994

  An tsare Paulos Eyassu da Isaac Mogos da kuma Negede Teklemariam a kurkuku ba tare da an yi musu shari’a ko kuma an tuhume su da wani laifi ba kuma suna kurkuku har wa yau.

 15. 1940 zuwa 1949

  Mutane na farko da suka zama Shaidun Jehobah a kasar Eritiriya.

  Domin ka ga jerin duka Shaidun Jehobah da aka tsare a kurkuku a Eritiriya saboda imaninsu, ka danna wannan adireshi.