Koma ka ga abin da ke ciki

11 GA YUNI, 2015
AZARBAIJAN

Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani

Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani

Shaidun Jehobah suna kira ga kasashen duniya da su dauki mataki a kan yadda aka tsare Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova ba bisa ka’ida ba. An tsare matan a kurkuku tun ranar 17 ga Fabrairu, 2015, sa’ad da Kotun Gunduma da ke yankin Sabail ya hukunta su da daurin watanni uku a inda ake tsare masu jiran shari’a domin ana tuhumarsu da laifin rarraba littattafan addini ba tare da izini ba. A kwanan nan kotun ya kara musu watanni biyu a kurkuku.

Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova

Ana Wulakanta Mata Masu Bin Doka Kamar Masu Aikata Miyagun Laifuffuka

A ranar 5 ga Disamba, 2014, Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova suna wa’azi a wani gida a birnin Baku sai ’yan sanda suka kama su. ’Yan sandan suka sake su bayan awoyi kadan, amma sau da yawa bayan haka an kiransu a ofishin ’yan sanda don a yi musu tambayoyi. A ranar 17 ga Fabrairu, 2015, Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (MNS) ta kai matan nan kotu su kadai don a hukunta su a matsayin masu aikata laifi. Alkalin ya ce suna yi wa “jama’a barazana” don ya sami hujjar saka su a inda ake tsare masu jiran shari’a. Nan da nan, sai MNS ta kai matan kurkuku a hedkwatarsu da aka nuna a sama.

Tun daga lokacin, ma’aikatan MNS suna zuwa yin bincike mai tsanani a gidajensu, kuma sun kwace littattafan addini da littattafan rubutu da kwamfutar tafi-da-gidanka da kuma wayar salula. Kotun ya ki duk wani kara da aka daukaka a madadin matan kuma bai yarda a tsare su a gida a maimakon inda ake tsare masu jiran shari’a ba.

Damuwa a Kan Lafiyar Matan

Lauyoyi da iyalai da kuma abokan matan sun nuna damuwarsu a kan yanayin lafiyar matan, wanda a ganinsu yana dada muni. Malama Zakharchenko tana da shekaru 55, kuma likitoci sun dauke ta nakasashiya domin ciwon sanyin kashi mai tsanani da ke damunta da kuma wani rauni da ta ji a kafa kafin wannan lokacin.

Kari ga haka, ana damuwa a kan yadda wannan yanayin zai shafi hankalin matan. MNS ba ta barin kowa ya ziyarce su sai lauyoyinsu kawai, kuma tana barin danginsu su aika musu da sutura da magunguna da kuma sabulun wanka sau daya kawai a wata. Danginsu sun yi kokari su aika musu da Littafi Mai Tsarki domin su ta’azantar da su, amma MNS ta ki sam-sam.

Shin Azerbaijani Za Ta Amince Cewa Kowa Na da ’Yancin Bin Addinin da Ya Ga Dama?

MNS ta tuhumi Shaidun Jehobah guda 20 sa’an nan ta binciki akalla gidaje goma a kan tana binciken Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova. Kari ga haka, wasu ma’aikata da suke wakiltar MNS da wakilan State Committee for Work with Religious Associations da ’yan sanda sun yi bincike a Majami’ar Mulki inda matan suke zuwa ibada.

Tun da yake hukumomin Azerbaijani sun ki su ba matan damar yin aikin farar hula, Shaidun Jehobah sun rubuta afil ga Office of the High Commissioner for Human Rights, (Babban Ofishin Kwamishina na Kare Hakkin Dan Adam) kuma sun tuntubi wasu kungiyoyi a kasashen duniya da su dauki mataki a kan yadda kasar Azerbaijani ta tsare Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova ba bisa ka’ida ba da kuma yadda ake wulakanta su a kurkuku. Kasar Azerbaijani ta sa hannu a yarjejeniyar daukaka hakkin kowane dan Adam kuma tana da’awar cewa ita kasa ce mai daukaka ’yancin addini.

Shaidun Jehobah suna bukatar gwamnatin Azerbaijani ta cika yarjejeniyar da ta yi na ba kowane dan kasarta ’yancinsa kuma ta bar Shaidun Jehobah su yi ibadarsu cikin salama. Suna rokon gwamnatin Azerbaijani ta saki wadannan matan nan da nan.