Koma ka ga abin da ke ciki

Labaran Shari’a a Armeniya

5 GA NUWAMBA, 2013

Armeniya Ta Ba Wadanda Suka Ki Shiga Soja Wani Aiki

Kamar dai idon gwamnatin Armeniya ya bude yanzu da ta soma amincewa da ’yancin da mutane suke da shi na ki da aikin soja saboda imaninsu. An ba wasu Shaidun Jehobah damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja.