Koma ka ga abin da ke ciki

NAGORNO-KARABAKH

An Kai Su Kurkuku Saboda Imaninsu

An Kai Su Kurkuku Saboda Imaninsu

Yankin Nagorno-Karabakh yana tsare Shaidun Jehobah da suka isa su shiga soja amma sun ki yin hakan saboda imaninsu. Gwamnatin ba ta amince da ’yancin kin shiga soja saboda imani ba kuma ba ta yi wani tanadin aikin farar hula a maimakon wannan ba. Saboda haka, ana tsare matasa Shaidun Jehobah a kurkuku domin sun ki su yi fada.

Kokarin Samun Izinin Yin Aikin Farar Hula a Maimakon Aikin Soja Bai Yi Nasara Ba

A ranar 29 ga Janairu, 2014, hukumar Askeran City Military Commissariat ta kira Artur Avanesyan wani Mashaidin Jehobah, ya yi aikin soja. Washegari sai Mr. Avanesyan ya rubuta afilkeshan zuwa Nagorno-Karabakh Military Commissariat don a ba shi damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja. Lauyansa ya sami ma’aikatan Nagorno-Karabakh da na Armeniya kuma aka soma yunkurin ba Mr. Avanesyan damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja a Armeniya.

Mr. Avanesyan ya kaura zuwa Armeniya don yana ganin kamar zai yi nasara kuma ya rubuta afilkeshan don aikin farar hula zuwa ga Masis Military Commissariat na Jamhuriyar Armeniya a ranar 13 ga Fabrairu, 2014. Amma a ranar 14 ga Yuli, 2014 yayin da Mr. Avanesyan yake jiran lokacin da zai bayyana a gaban hukumar ba da aikin farar hula na Armeniya, sai aka kira shi ya je ofishin ’yan sanda da ke Yerevan. Sa’ad da ya isa ofishin, ya ga ’yan sanda daga Nagorno-Karabakh suna jiransa. Sai suka kama shi suka kai shi Nagorno-Karabakh. Washegari aka kai shi inda ake tsare masu jiran shari’a kuma aka yi masa shari’a a First Instance Court na Nagorno-Karabakh.

Sa’ad da ake yi masa shari’a sai ya ji cewa watanni hudu da suka wuce, kotun ta ba da izini a tsare shi kuma ta ba da doka a kai shi kurkuku yayin da yake jiran shari’a. Kotun ya tsaya a kan shari’ar da ya yanke da farko kuma aka kai Mr. Avanesyan kurkuku nan da nan. Kotun ya ki amincewa da afil da aka yi cewa a sake shi kafin lokacin shari’ar.

A ranar 30 ga Satumba, 2014, kotun ya yanke wa Mr. Avanesyan hukuncin dauri na tsawon watanni 30 a kurkuku. An daukaka karar a kotu amma Kotun Daukaka Kara ya tsaya a kan hukuncin da aka yanke. Bayan haka Mr. Avanesyan ya daukaka karar a Kotun Koli da ke Nagorno-Karabakh a ranar 25 ga Disamba, 2014, amma Kotun ya yarda da hukuncin dayan kotun.

Har zuwa yau yankin Nagorno-Karabakh yana tsare matasa maza domin suna bin imaninsu. Ta yin hakan, wannan yankin ya keta ka’idodin da aka kafa a duk duniya na ba wa masu kin aikin soja damar yin aikin farar hula saboda imaninsu.

Jerin Shekaru

 1. 25 ga Disamba, 2014

  Kotun Koli da ke Nagorno-Karabakh ya tsaya a kan hukuncin da aka yi wa Artur Avanesyan.

 2. 30 ga Satumba, 2014

  Martakert, First Instance Court na Nagorno-Karabakh ya yanke wa Artur Avanesyan hukuncin dauri na tsawon watanni 30 a kurkuku.

 3. 14 ga Yuli, 2014

  An kama Artur Avanesyan a Armeniya kuma aka kai shi yankin Nagorno-Karabakh, inda ake tsare masu jiran shari’a.

 4. 30 ga Disamba, 2011

  An yi wa Karen Harutyunyan wani Mashaidin Jehobah mai shekara 18 hukuncin dauri na watanni 30 a kurkuku domin ya ki shiga soja.

 5. 16 ga Fabrairu, 2005

  An tsare wani Mashaidin Jehobah mai suna Areg Avanesyan a kurkuku domin ya ki shiga soja kuma an yanke masa hukuncin dauri na watanni 48.

 6. 12-13 ga Yuni, 2001

  An tsare wasu Shaidu guda uku a kurkuku na tsawon watanni shida zuwa shekara guda domin sun ki a yi musu horo a matsayin sojoji.

  Domin ka ga jerin duka Shaidun Jehobah da aka tsare a kurkuku a yankin Nagorno-Karabakh saboda imaninsu, ka danna wannan adireshi.