Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

3 GA YUNI, 2015
RASHA

Ma’aikatar Shari’a a Birnin Moscow Ta Yi wa Shaidun Jehobah Rajista

Ma’aikatar Shari’a a Birnin Moscow Ta Yi wa Shaidun Jehobah Rajista

A ranar 27 ga Mayu, 2015, Russian Federation Ministry of Justice ta yi rajistar kungiyar Shaidun Jehobah da ke Moscow. An yi wannan rajistar shekaru biyar bayan da Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya ce matakin da kotun da ke Moscow ya dauka na wargaje kungiyar Shaidun Jehobah ba bisa ka’ida ba ne.

Bayan an yi shekaru ana shari’a, Golovinskiy District Court of Moscow ya yanke hukuncin wargaje kungiyar Shaidun Jehobah a shekara ta 2004. A shekara ta 2010, Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya ba da doka cewa Rasha ta sake yi wa kungiyar rajista kuma ta biya ta diyya domin barnar da ta yi. Gwamnatin Rasha ta biya diyyar, amma sai yanzu ne ta yi rajistar kungiyar a yankin.