Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

12 GA AFRILU, 2016
AZARBAIJAN

’Yan Sanda a Azerbaijani Sun Dakatar da Wani Taron Tuna da Mutuwar Yesu

’Yan Sanda a Azerbaijani Sun Dakatar da Wani Taron Tuna da Mutuwar Yesu

Ba zato ba tsammani ’yan sanda a Gakh suka dakatar da taron Tuna da Mutuwar Yesu da aka yi a ranar 23 ga Maris, 2016, taro na musamman da Shaidun Jehobah suke yi kowace shekara. An yi taron a gidan wani Mashaidi ne. ’Yan sandan sun nuna wata takarda da ta yi kama da takardar shaida daga kotu, wadda ta ba su izinin yin bincike, kuma da hakan suka kwace wasu littattafan addini har da Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, ’yan sandan suka kwashi dukan wadanda suka halarci taron zuwa ofishin ’yan sanda da ke yankin, suka tuhume su kuma suka tilasta musu su rubuta shaidarsu. ’Yan sandan sun saki wadanda suka kama bayan sun tsara dokokin da za su iya sa a kama maza shida daga cikinsu da laifi a karkashin tsarin dokoki na Administrative Violations Code.