Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

14 GA YULI, 2015
AZARBAIJAN

Azerbaijani Ta Kara Zaman Kurkuku da Ba Bisa Ka’ida Ba Har Tsawon Watanni Biyu

Azerbaijani Ta Kara Zaman Kurkuku da Ba Bisa Ka’ida Ba Har Tsawon Watanni Biyu

A ranar 4 ga Yuli, 2015, Kotun Gunduma da ke yankin Sabail ya kara zaman kurkuku da tsawon watanni biyu wa Shaidun Jehobah guda biyu da suke jira a yi musu shari’a. Hakan ya sa ba za a saki Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova ba har sai 17 ga Satumba, 2015. Masu bincike suna da’awar cewa yana da kyau a ci gaba da tsare su yayin da ake shirya kararsu.

Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (MNS) ta tsare matan nan ba bisa ka’ida ba a ranar 17 ga Fabrairu, 2015, a lokacin da suke tattauna Littafi Mai Tsarki da makwabtansu. Kari ga haka, MNS ta ci gaba da tuhumar Shaidu dabam-dabam a kan wannan shari’ar, wasu ma fiye da sau daya.