Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

2 GA YULI, 2015
RUWANDA

Kotun Ruwanda Ya Amince da Kasancewar Addinai Dabam-dabam

Kotun Ruwanda Ya Amince da Kasancewar Addinai Dabam-dabam

Wani kotu a yankin Karongi a Ruwanda ya goyi bayan ’yancin addini wa dalibai takwas da Shaidun Jehobah. Batun da ya taso shi ne cewa sun ki su saka baki a koyarwar wani addini dabam saboda lamirinsu.

Yawancin makarantu a Ruwanda addinai ne suka kafa su. A cikin wadannan makarantun ana bukatar dalibai su sa hannu a hidimomin addinan kuma su biya baikonsu. Daga shekarar 2008 zuwa 2014 an kore dalibai 160 wadanda Shaidun Jehobah ne daga makarantu saboda sun ki saka hannu a batun wani addini. Karar da aka kai a Karongi, a Yammacin Yankin ya nuna cewa gwamnatin Ruwanda za su iya warware matsalarsu idan suka amince da addinai dabam-dabam.

Batun Bambancin Addini Ne Ke Sa Makarantu Su Kori Yara Daga Makaranta

A ranar 12 ga Mayu, 2014 shugabanin makarantar Groupe Scolaire Musango a Karongi sun kori yara Shaidun Jehobah takwas ’yan shekara 13 zuwa 20, * daga makarantar saboda sun ki su saka hannu a hidimomin addini. Iyayen sun kai karar wannan batun a wurin gwamnati da ke kula da yanki Rwankuba a kasar sai aka ce yaran su koma makaranta. Domin makarantar ba su gamsu da umurnin gwamnati na cewa yaran su koma makaranta ba, sai suka kulla cewa yaran ba su da ladabi sa’ad da ake taken kasa domin ba sa yinsa. A ranar 4 ga Yuni, 2014, bayan kwana biyu da yaran suka koma makaranta, sai ’yan sanda suka je makarantar suka kama yaran.

’Yan sandan sun tsare yaran na kwana shida. ’Yan sandan suka yi wa yaran ashar kuma suka yi wa manya biyun duka wai su ne ke sa kananan taurin kai. Amma duk da irin wannan wulakanci, yaran nan takwas suka ki su yi rashin imani.

Kotu Ya Ba Wa ’Yan Makaranta ’Yanci

A ranar 9 ga Yuni, 2014 ’yan sandan suka fitar da dalibai bakwai, amma wadanda suka kai karar sun ’yantar da karamin yaron daga batun gabaki daya. Har ila, ’yan sandan ba su saki babban cikinsu ba har na kwanaki tara. Sai alkalin ya ce a fitar da shi har sai ranar da za su sake zuwa kotu a ranar 14 ga Oktoba, 2014.

Sa’ad da suka kai kotun, alkalin ya yi wa kowannensu tambayoyi. Daya daga cikinsu ya bayyana wa alkalin dalilin da ya sa aka kore su a makaranta, ya ce, ba saboda sun ki yin taken kasa ba ne amma cewa sun ki su biya baiko ne na coci da hidimomin addini da ake yi a makarantar.

Wannan ya sa alkalin ya ce makarantar su kawo shaidar karin bayani game da batun da suka ce yaran ba su “yi ladabi da yin taken kasa ba.” Sa’ad da makarantar ta matsa wa daliban, sai suka gaya musu cewa yaran ba su yi rashin ladabi ba sa’ad da ake taken kasa.

An fito da shawarar da kotun Karongi ya yanke a ranar 28 ga Nuwamba, 2014, cewa kin yin taken kasa “ba rashin biyayya ba ne ko rashin ladabi ga kasa.” Dokar da kotun ya kafa yanzu ya ba wa yaran ’yanci kuma zai taimaka a amince da kasancewar addinai dabam-dabam a makarantu na kasar Ruwanda.

An Yi Roko Don a Girmama Cikakken ’Yanci

Shaidun Jehobah a Ruwanda sun yi farin ciki don ’yanci da suka samu bayan nasarar da yaran makarantar Groupe Scolaire Musango suka yi. Amma a wasu lokuta a kan kori yaran Shaidun Jehobah a makaranta domin abin da suka yi imani da shi, kuma hakan na sa su bar makarantar zuwa wani. Wasu yaran fa an bar su ba makaranta domin an kore su daga makarantar gwamnati.

Shaidun Jehobah suna son yaransu su yi makaranta yadda saura yara ke yi. Suna son yaransu su sami fasaha da zai taimaka musu a rayuwa, su zama nagargaru a yanki da suke zama. Shaidun Jehobah suna sa rai cewa nasarar da suka yi a kotun da ke Karongi zai sa dukan makarantu na Ruwanda su fara girmama ’yancin addini da lamirin yara a makarantarsu.

^ sakin layi na 5 Yawancin mutane a Ruwanda shekarunsu 21 (Talifi na 360 na Dokar Kasar).