Koma ka ga abin da ke ciki

Labaran Shari’a da Hakkin ’Yan Adam

GEORGIA

Shaidun Jehobah Sun Yi Kamfen na Ilimantar da Mutane Game da Hukuncin ECHR a Georgia

A watan Afrilu 2015, kamfen da aka yi ya sanar da ’yan doka hukuncin da ECHR ya yanke a kwanan nan kuma zai taimaka musu su san hidimomin Shaidun Jehobah.

KIRGIZISTAN

Lokacin Daukan Mataki Mai Muhimmanci a Kan ’Yancin Addini a Kyrgyzstan

A ranar 24 ga Disamba, 2014, Kotun Koli ya daukaka ’yancin da ’yan kasa suke da shi na bayyana wa wasu abin da suka yi imani da shi, har da Shaidun Jehobah. Shin Shaidun Jehobah a kudancin Kyrgyzstan za su iya samun ’yancin addini yanzu?

ARMENIYA

Armeniya Ta Ba Wadanda Suka Ki Shiga Soja Wani Aiki

Kamar dai idon gwamnatin Armeniya ya bude yanzu da ta soma amincewa da ’yancin da mutane suke da shi na ki da aikin soja saboda imaninsu. An ba wasu Shaidun Jehobah damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja.

KOREA TA KUDU

Rashin Adalci a Kasar Koriya ta Kudu ta Jawo Rashin Amincewar Kasashen Duniya

Sabuwar kasida da Shaidun Jehobah suka wallafa ta bayyana rashin adalci da ake yi wa darurruwan matasa da suka ki aikin soja a kan imaninsu ta wajen tsare su a kurkuku.