Koma ka ga abin da ke ciki

Labaran Shari’a da Hakkin ’Yan Adam

YUKARAN

An Kai Musu Hari Domin Imaninsu a Gabashin Ukraine

Mutane dauke da makamai sun saci Shaidun Jehobah guda 26 kuma sun gana musu azaba domin su ba ’yan addinin Orthodox ba ne kuma ba ruwansu da siyasa. Shaidun sun ki su musanta imaninsu.

RUWANDA

Kotun Ruwanda Ya Amince da Kasancewar Addinai Dabam-dabam

Wani Kotu a yankin Karongi a Ruwanda ya goyi bayan ’yancin addini wa dalibai takwas da Shaidun Jehobah ne. Shawarar da kotun ya yanke zai iya taimaka a amince da kasancewar addinai dabam dabam a makarantu na kasar Ruwanda kuwa?

AZARBAIJAN

Shaidu Sun Yi Kira da A Saki Matan da Aka Tsare a Azerbaijani

Ana tsananta wa Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova kamar yadda ake yi wa masu laifi mai tsanani domin sun yi magana da wasu game da imaninsu. Shin, Azerbaijani za ta nuna cewa tana daukaka ’yancin addini kamar yadda take da’awa?

AZARBAIJAN

Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani

Shin Azerbaijani za ta ba kowa ’yancin bin addini kamar yadda take da’awa ta wurin sake wadannan mata biyu, wato Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova, kuma ta bar Shaidun Jehobah su yi ibadarsu cikin salama?