Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

LABARAI DAGA DUNIYA KEWAYE

Mun Kyautata Dandalinmu na Yanar Gizo

Mun Kyautata Dandalinmu na Yanar Gizo

A cikin ’yan watanni da suka shige, rukunin Shaidun Jehobah 40 a New York sun yi aiki sosai tare da sashen Fasaha da na Rubuce-Rubuce su sake kyautata dandalinmu na yanar gizo, wato, www.jw.org kuma ta zama da sauƙin shiga da fita a kan kamfuta ko kuma cikin wayar jin magana. Ban da haka, sun yi wa dandalin yanar gizon canja canje, da makasudai biyu.

1. Don a haɗa dandalinmu na yanar gizo. Dandalin yanar gizo uku da Shaidu suke da shi za a haɗa su ta zama guda da ake aiki da shi, wato,—www.jw.org. Sauran biyun, www.watchtower.org da www.jw-media.org, za a daina amfani da su. Rage Yanar Gizon zai taimaka a iya bincike a dandali ɗaya idan mutum yana bincike game da Shaidu. Alal misali, za ka iya shiga, ka saurara, ko kuma buga shafofin Littafi Mai Tsarki da wasu littattafai a harsuna da yawa.

2. Don Ƙarin sanarwa. Dandalin yanar gizo da aka gyara yana ɗauke da taƙaitattun amsoshin tambayoyin Littafi Mai Tsarki kuma yana zance game da aikin wa’azi, ofisoshin reshe, Majami’un Mulki da kuma taron gunduma na Shaidun Jehobah. Akwai sashen “Labarai” a kan aukuwa da suka shafi Shaidun Jehobah a duk duniya. Akwai kuma sashe domin iyalai, yara masu shekaru daga goma sha uku, da kuma yara ƙanana.

A kowace rana, mutane ɗarurruwan dubbai mutane da yawa suna karatun littattafan Shaidun a waya cikin harsuna 430. Suna sauke kusan rabin miliyan na muryoyi, EPUB, PDF, ko kuma a bidiyo na yaren kurame. Kowace rana, ɗarurruwan mutane suna biɗan wani ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su.