Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

MAY 2, 2017
AJANTINA

Ruwan Sama Ya Yi Bala’in Barna a Ajantina

Ruwan Sama Ya Yi Bala’in Barna a Ajantina

BUENOS AIRES, Ajantina​—Daga ranar 29 ga Maris, 2017, har zuwa 9 ga Afrilu, 2017, an yi bala’in ruwan sama da ya jawo ambaliya a garuruwan Buenos Aires, Chaco, Chubut, Catamarca, Jujuy, Misiones, La Pampa, Salta, San Juan, Santa Cruz, Santa Fe, Santiago del Estero, da kuma Tucumán a kasar Ajantina. Ofishin Shaidun Jehobah da ke Ajantina ya cewa babu wani cikin Shaidun Jehobah da ya rasa ransa ko ya ji wani rauni a sakamakon wannan bala’’in.

Jihohin da wannan bala’in ruwan sama ya fi yin barna su ne Chubut da kuma Salta. An kwatanta ruwan sama da aka yi cikin ‘yan kwanaki kadan a birnin Comodoro Rivadavia, Chubut da yawan ruwan sama da ake yi a cikin shekara daya, hakan ya sa Shaidun Jehobah fiye da 60 sun fita tare da iyalansu kuma bar gidajensu. Kari ga haka, Majami’un Mulki biyu sun lalace a Chubut, da kuma daya a Salta. Ofishin Shaidun Jehobah da ke Ajantina ya kafa kwamitin tara kayan agaji a Chubut da kuma Salta don su kula da gayan agajin da ake kawowa, kuma hakan zai dauki makonni da yawa.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Argentina: Omar A. Sánchez, +54-11-3220-5900