Koma ka ga abin da ke ciki

8 GA YUNI, 2018
RASHA

Matan Shaidun Jehobah da aka saka a kurkuku a Rasha sun tura wa mashawarci Putin

Matan Shaidun Jehobah da aka saka a kurkuku a Rasha sun tura wa mashawarci Putin

A safiyar ranar 8 ga Yuni, 2018, mata goma na Shaidun Jehobah 17 da aka saka a kurkuku a kasar Rasha sun tura wasika ga mai ba shugaba Putin shawara mai suna Mikhail Fedotov da kuma shugaban Majalisar Kāre Hakkin Bil Adama da ’Yancin Ɗan Adam.