Koma ka ga abin da ke ciki

Dan’uwa da ’Yar’uwa Polyakov (a hagu), ’Yar’uwa Bektemirova (a sama ta dama), da kuma ’Yar’uwa Dyusekeyeva (a kasa ta dama)

25 GA SATUMBA, 2020
RASHA

Ana Shirin Yin Shari’a a Kan Ma’aurata na Farko da Aka Tsare a Rasha Tun Ba A Yi Musu Hukunci Ba, Tare da Wasu ’Yan’uwa Mata Biyu

Ana Shirin Yin Shari’a a Kan Ma’aurata na Farko da Aka Tsare a Rasha Tun Ba A Yi Musu Hukunci Ba, Tare da Wasu ’Yan’uwa Mata Biyu

Ranar da Za A Yanke Hukuncin

A ranar 21 ga Oktoba, 2020, * Kotun Gundumar Pervomayskiy da ke Birnin Omsk zai sanar da hukuncinsa a kan karar da aka shigar game da Dan’uwa Sergey Polyakov da matarsa, Anastasia, da kuma ’Yar’uwa Gaukhar Bektemirova da ’Yar’uwa Dinara Dyusekeyeva. Wanda ya shigar da karar yana so kotun ya yanke wa Dan’uwa Polyakov hukuncin dauri na tsawon shekara shida da rabi a kurkuku. ’Yan’uwa mata ukun kuma, yana so a yi shekara biyu ana sa musu ido.

Karin Bayani

Sergey Polyakov

  • Shekarar Haihuwa: 1972 (Yankin Murmansk)

  • Tarihi: Ya je makarantar jami’a kuma ya kware wajen yin amfani da wani irin haske da ake kira radiophysics, don yin magani. Ya auri Anastasia a 2003

Anastasia Polyakova

  • Shekarar Haihuwa: 1984 (Yankin Murmansk)

  • Tarihi: Ta yi karatu a matsayin lauya a jami’a. Ita da maigidanta Sergey suna jin dadin koyan yaruka dabam-dabam kamar, yaren Chinese da Kazakh da Serbian da kuma Yaren Kurame na Rasha

Gaukhar Bektemirova

  • Shekarar Haihuwa: 1976 (Uryl, Kazakhstan)

  • Tarihi: Ita ce ’yar auta cikin yara shida. Ta yi girma a yankunan tuddai da ke Kazakhstan kuma tana sha’awar abubuwan da Allah ya halitta. Ta yi shekaru tana tunanin dalilin da ya sa muke rayuwa a duniya. Sai da ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki ne ta sami amsoshin tambayoyin da ke damun ta. Kari ga haka, ta sami karfafa da kuma karfin jimre yadda aka daure ta, ta wajen yin nazarin Kalmar Allah sosai

Dinara Dyusekeyeva

  • Shekarar Haihuwa: 1982 (Leningradskoye, Kazakhstan)

  • Tarihi: Sa’ad da take karama, ta yi tunani sosai a kan dalilin da ya sa muke rayuwa a duniya. Ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da take shekara 17. Ta yi murna sosai sa’ad da ta ga shawarwari masu kyau da ke Littafi Mai Tsarki da kuma sunan Mawallafinsa wato, Jehobah a ciki. Tana jin dadin buga wasan kwallon kwando, da wasan kwallon raga ta volley, da tsere, da kuma tuka keke

Yadda Labarin Ya Soma

A daren 4 ga Yuli, 2018, ’yan sanda sun bude kofar gidan Dan’uwa Polyakov karfi da yaji kuma suka shiga sa’ad da ma’auratan suke barci. ’Yan sandan sun rufe fuskokinsu kuma sun dūki Dan’uwa Polyakov sosai. Sai suka kama ma’auratan kuma suka kai su kurkuku ba tare da an yi musu shari’a ba. Su ne ma’aurata na farko da aka kai su kurkuku bayan da Kotun Koli ya haramta ayyukan Shaidun Jehobah a 2017. An kulle Dan’uwa Polyakov a wani wuri shi kadai, matarsa kuma a wani wuri dabam ita kadai har tsawon wata biyar. Daga baya, sun koma gida amma an hana su barin gidansu har tsawon wata uku.

A Mayu 2019, jami’an tsaro sun sake shiga gidajen Shaidun Jehobah a yankin Omsk ba bisa ka’ida ba. A lokacin ne aka kama ’Yar’uwa Bektemirova da ’Yar’uwa Dyusekeyeva. Sa’an nan aka hada kararsu da na Dan’uwa Polyakov da matarsa. An soma sauraron karar dukansu a 1 ga Afrilu, 2020.

Mun tabbata cewa Jehobah zai ba wa bayinsa karfin jimre irin wannan rashin adalcin.​—Afisawa 3:20.

^ sakin layi na 3 Za a iya canja ranar