Koma ka ga abin da ke ciki

4 GA AGUSTA, 2017
NIJERIYA

Ruwan Sama Mai Karfin Gaske a Najeriya

Ruwan Sama Mai Karfin Gaske a Najeriya

An yi ruwan sama mai karfin gaske a kudancin Nageriya daga ranar 6-12 na Yuli 2017, kuma hakan ya jawo ambaliya a jihar Legas da Niger da kuma Oyo. Rahotanni sun nuna cewa a kalla mutane 18 ne suka mutu sanadiyyar ambaliyar.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke Najeriya ya tabbatar da cewa ba Mashaidin da ya rasa ransa ko kuma ya ji rauni a ambaliyar amma mutane hudu sun bar gidajensu. Kari ga haka, gidajen Shaidun Jehobah guda biyu ne suka lalace kuma gidan daya ya rushe. Shaidun Jehobah a Najeriya suna tallafawa mambobinsu da ambaliyar ta shafa, har da makwabtansu da ba Shaidu ba da suka bar gidajensu ko suka rasa gidajensu.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Nigeria: Paul Andrew, +234-7080-662-020