Koma ka ga abin da ke ciki

20 GA SATUMBA, 2017
MEZIKO

Mahaukaciyar Guguwar Max ta Auku a Kudancin Mezico

Mahaukaciyar Guguwar Max ta Auku a Kudancin Mezico

A ranar 14 ga Satumba, 2017, mahaukaciyar guguwar Max ta auku a tekun kudancin kasar Meziko kuma daga baya guguwar ta zama iska mai karfi sosai. Guguwar ta sa an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya kuma hakan ya jawo ambaliyar da ta yi barna sosai.

Har yanzu ana bincike don a san irin barnar da ambaliyar ta yi a yankunan da ke kasar. Abin takaici an gano cewa wani dan’uwa ya rasa ransa a lokacin guguwar, yayin da yake kokarin ya taimaka wa makwabcinsa. ’Yan’uwan da ke ofishinmu da ke Meziko, suna aiki tare da ’yan’uwa a kasar don su tallafa ma wadanda guguwar ta shafa.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Mexico: Gamaliel Camarillo, +52-555-133-3048