Koma ka ga abin da ke ciki

8 GA SATUMBA, 2017
MEZIKO

An Yi Girgizar Kasa a Meziko

An Yi Girgizar Kasa a Meziko

A ranar Alhamis 7 ga Satumba, wata girgizar kasa mai karfin awo 8 da digo 2 ta afka wa tekun Fasifik da ke kudancin kasar Meziko. Ba a taba yin irin wannan girgizar kasa ba, kuma ta kashe akalla mutane 45 a Meziko. Mun yi bakin ciki da muka samu rahoto cewa wani dan’uwa da ‘yan’uwa mata biyu suna cikin wadanda suka mutu.

Kari ga haka, mun sami rahoto cewa gidajen ‘yan’uwa da kuma Majami’un Mulki da yawa sun lalace. Majami’un Manyan Taro biyu da ke Chiapas State sun lalace. Ana kan bincika irin barnar da girgizar kasar ta yi.

Mun ci gaba da yi wa ‘yan’uwanmu addu’a da tabbaci cewa Jehobah zai yi musu ta’aziyya kuma ya karfafa su.​—⁠2 Tasalonikawa 2:​16, 17.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Mexico: Gamaliel Camarillo, +52-555-133-3048