Koma ka ga abin da ke ciki

Motocin da aka cin na wa wuta a lokacin da ake fada a Culiacán

8 GA NUWAMBA, 2019
MEZIKO

An Kashe Wani Mashaidi Sa’ad da Ake Fada a Culiacán Meziko

An Kashe Wani Mashaidi Sa’ad da Ake Fada a Culiacán Meziko

A ranar 17 ga Oktoba, 2019, ’yan sanda da jami’un tsaro sun yi musanyar wuta da manyan ’yan daba da ke sayar da kwayoyi a birnin Culiacán Sinaloa da ke kasar Meziko wanda kusan mutane miliyan daya ne ke zama a birnin. ’Yan daban na rike da manyan makamai. A lokacin wannan harbe-harben, an rufe manyan hanyoyi, an kona motoci, kuma fursunoni a kurkukun da ke kusa da wurin sun gudu. Jami’un sun ba da rahoto cewa akalla mutane goma sha hudu ne aka kashe. Abin takaici, ’yan’uwanmu da ke reshen ofishi da ke Amirka na Tsakiya sun ba da rahoto cewa dan’uwanmu mai suna Noé Beltrán yana cikin wadanda suka mutu sanadiyyar wannan fada.

Dan’uwa Noé Beltrán da yaransa biyu

Dan’uwa Beltrán yana da yara uku kuma shekararsa 39, yana wurin aiki sa’ad da harsashi ya same shi. ’Yan’uwa maza da mata tare da mai kula da da’ira suna ta’azantar da kuma karfafa matarsa mai suna Rocío da kananan yaransu.

Da akwai masu shela guda 7,000 da kuma ikilisiyoyi 80 a birnin Culiacán. A lokacin fadan, wadansu ikilisiyoyi sun canja lokacin taronsu na tsakiyar mako da kuma taron fita wa’azi. Wasu ’yan’uwa kuma sun yin amfani da na’ura don su saurari taron tsakiyar mako a gidansu. ’Yan’uwa masu kula da da’ira suna karfafa ’yan’uwan da wannan bala’i ta tsorata.

Muna matukar bakin ciki don mutuwar Dan’uwa Beltrán, kuma muna addu’a Jehobah ya ci gaba da taimaka wa ’Yar’uwa Beltrán da yaransu. Muna dokin ganin lokacin da za a yi zaman lafiya a duniya, kuma maimakon a rika bakin ciki za a rika farin ciki sosai.​—Markus 5:42.