Koma ka ga abin da ke ciki

Dakta Gabriele Hammermann, direktan Sansanin Dachau, ta nuna hoton allon na tuna da Dan’uwa Max Eckert a lokacin da take yin jawabi.

9 GA YULI, 2018
JAMUS

Taron Tunawa da Dan’uwa Max Eckert Wanda Ya Mutu a Kurkuku

Taron Tunawa da Dan’uwa Max Eckert Wanda Ya Mutu a Kurkuku

A wani bikin da aka yi a ranar 7 ga Mayu, 2018 a Dachau Concentration Camp Memorial Site, an bude wani allo a a gaban mutane kusan 200 domin tunawa da dan’uwa Max Eckert. An sa shi a kurkuku a Dachau har na tsawon shekara biyu kafin aka kaurar da shi zuwa kurkukun Mauthausen a kasar Austriya. Bai sake dawowa gida ba. Ko da yake mutane kalilan ne suka san Dan’uwa Eckert kafin ya mutu, yanzu mutane da yawa sun san cewa shi mutum ne mai aminci sosai.

Hoto na kwanan nan na sansanin Dachau wurin da aka saka Dan’uwa Max Eckert a kurkuku kafin a tura shi Mauthausen.

Sansanin Mauthausen da Max Eckert ya mutu.

Rahotanni game da Dan’uwa Eckert sun nuna cewa shi mutum ne mai aminci. A shekara ta 1985 an ci tarar shi da matarsa domin suna yin wa’azi. Daga baya, an kore shi daga aiki domin ya ki rike tutar Nazi a Jamus. A shekara 1937, ya zama daya daga cikin kwararrun Shaidu 600 da aka tsare a kurkuku ba tare da shari’a ba a Dachau. Bayan shekaru biyu sai aka sauya masa kurkuku zuwa Mauthausen inda a kalla fursunoni 90,000 suka rasa rayukansu don tsananin azaba. A ranar 21 na watan Fabrairu 1940, matar Eckert ta sami sako cewa: “Mijinki ya rasu a kurkuku yau. Don karin bayani, ki tuntubi ’yan sanda.” Dan’uwa Eckert ya mutu yana dan shekara 43.

A wurin bikin gabatarwar, Dakta Gabriele Hammerman, direktan wannan kurkuku na Dachau ta yi bayani cewa “an tsananta wa Daliban Littafi Mai Tsarki [yadda ake kiran Shaidun Jehobah a lokacin] domin ba sa zama memban kungiyoyin Nazi domin imaninsu. Ban da haka, ba sa sara wa tuta ko kuma shiga aikin soja.” Ta kara da cewa: “Wadanda suke kurkuku tare da su a dā sun mutunta halayen daliban Littafi Mai Tsarki. Sun ambata amincin su da kuma halin son taimaka wa mutane.”

Kakakin Shaidun Jehobah a Jamus, Dan’uwa Wolfram Slupina ya tabbatar cewa mutane da yawa da suka halarci bikin ba su san dan’uwa Eckert, ya ce: “Ba mu da hoton Max Eckert.” Amma ya ce wannan allon “ya nuna cewa Dan’uwa Eckert mai aminci ne kuma ya kuduri niyya ba zai bar bin imaninsa ba, ko da hakan zai sa a kashe shi.

Babu shakka, Jehobah yana tuna da bangaskiya da amincin Max Eckert, da kuma sauran Shaidun Jehobah da suka mutu domin imaninsu.​—Ibraniyawa 6:10.