Koma ka ga abin da ke ciki

28 GA MARIS, 2018
LABARAN DUNIYA

Nuna Hadin Kai a Lokacin da Aka Yi Kamfen na Rubuta Wasika Zuwa Rasha

Nuna Hadin Kai a Lokacin da Aka Yi Kamfen na Rubuta Wasika Zuwa Rasha

A ranar Talata 21 ga Maris, 2017, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta umurce dukan mabiyanta su rubuta wasiku na rokon hukumomin gwamnatin da ke son saka wa aikinmu takunkumi a kasar Rasha. Duk da cewa ba za a iya kiyasta adadin wasiku da hukumomin suka samu ba, Shaidun Jehobah da yawa da suka tura wasika sun sami amsa cewa wasikarsu ta isa wurin hukumomin. Gwamnatin Rasha ta ki jin roko da aka yi, amma ta yi amfani da ikonta a hanyar da ba ta dace ba kuma ta hana Shaidun Jehobah da ke wurin yin ibada. Duk da haka, wasiku da Shaidu suka rubuta ya nuna irin hadin kai da kungiyar Jehobah take da shi. Kari ga haka, ya karfafa Shaidu da ke Rasha su ga cewa dukan ’yan’uwa a fadin duniya suna goyon bayansu kuma za su tallafa musu.​—1 Bitrus 2:17

Wata karamar yarinya a Boliviya ta sa hannu a wannan kamfen.

Shaidun Jehobah sun yi iya kokarinsu don saka hannu a wannan kamfen din. A wasu kasashe, tura wasika zuwa Rasha yana da tsada sosai, saboda haka, Shaidun Jehobah masu arziki sun tallafa ma talakawa don su ma su iya tura wasika zuwa Rasha. Wasu Shaidu kuma sun tura wasikunsu zuwa abokansu da ke wasu kasashen da tura wasika zuwa Rasha bai da tsada don su tura musu wasikar. Iyalai da kuma Shaidu a ikilisiyoyi sun hadu wuri daya don su rubuta wasikar kuma su tura wasikar tare. Yin hakan ya sa tura wasikar ta yi sauki, kuma ya sa Shaidu sun kusaci juna da kuma Jehobah. Hakan abu ne da ba za su taba mantawa ba.

Akwai rahotannin da suka nuna cewa har ma’aikata a wurin tura wasiku sun tallafa. Alal misali, manajan wani wurin aika wasika a birnin Barranquilla da ke Kolombiya, ya ce: “Irin hadin kan da kuke da shi da kuma yadda dukanku kuka rubuta wasika don abin da ke faruwa a Rasha, ya ba ni mamaki sosai. Ina tunanin yadda zai kasance a kowane birni a fadin duniya daga abin da kuke yi a Barranquilla. Ina fatan cewa mutane za su ga yadda wannan sakon yake da muhimmanci.” A garin Anseong a Koriya ta Kudu wani shugaban wurin tura wasika ya kirkiro wata hanya ta musamman wa Shaidun Jehobah don tura wasikun, har da wata ambulan da aka tsara ta masamman don aika sako kyauta zuwa kasar waje.

Shaidun Jehobah da ke wata ikilisiya a kasar Guinea sun rubuta wasiku tare.

Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna Yaroslav Sivulskiy ya ce: “Sa’ad da ’yan’uwa a Rasha suka ji cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun ce a yi kamfen na rubuta wasika a duk fadin duniya, hakan ya sa su san cewa ko da wane hukunci ne kotu ta yanke, suna da tabbacin cewa suna da masu goyon bayansu sosai.”

Dan’uwa Mark Sanderson memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ce: “Wannan kamfen na rubuta wasiku ya nuna a fili cewa Shaidun Jehobah tsintsiya-madaurinki-daya ne. Yayin da muke shiga kwanaki na karshe sosai, kasancewa da hadin ne zai taimaka mana mu tsira. Yayin da muke jiran lokacin da Jehobah zai dau mataki don abin da ke faruwa a Rasha, za mu ci gaba da yin iya kokarinmu don mu taimaka wa ’yan’uwanmu. Kuma za mu ci gaba da hada kai wajen yin addu’a ga Jehobah, da tabbacin cewa Ubangijinmu zai kula da su.”​—Zabura 65:2.

 

Austriya

Boliviya

Bosniya and Herzegovina

Denmark

Ecuador

Jamus

Gana

Guatemala

Indonesiya

Jafan

Nepal

Romaniya

Ruwanda

Sulobakiya

Sifen

Sri Lanka

Siwizalan

Tanzaniya

Zambiya