Koma ka ga abin da ke ciki

11 GA MAYU, 2018
LABARAN DUNIYA

Kauna ta Motsa ’Yan’uwa Su Yi Aikin Ba da Agaji a Tsibirai

Kauna ta Motsa ’Yan’uwa Su Yi Aikin Ba da Agaji a Tsibirai

Bidiyon da ke gaba na dauke da rahoto game da aikin da aka yi na ba da agaji bayan da Mahaukaciyar Guguwar Irma da Maria suka auko wa tsibiran da ofisoshinmu da ke Barbados da Faransa da kuma Amirka ke kula da su. A rahoton an nuna irin jar aikin da ’yan’uwan da suka ba da kansu suka yi don su taimaka. Kari ga haka, an ba da rahoto game da ziyarar da dan’uwa Mark Sanderson memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya kai da kuma ziyarar dan’uwa Gary Breaux mataimakin Kwamitin Hidima.