Koma ka ga abin da ke ciki

Benezuwela: Ana daukan muryar wata ’yar’uwa a yaren Warao (sama ta hagu), ’yan’uwa biyu daga cikin mafassaran yaren Piaroa suna aiki (kasa ta hagu). Koriya ta Kudu: Wasu sun taru suna kallon taron yanki na 2020 a matsayin iyali (dama)

4 GA SATUMBA, 2020
LABARAN DUNIYA

Taron Yanki na 2020​—Mafassara Sun Yi Aikinsu Duk da Matsaloli

Taron Yanki na 2020​—Mafassara Sun Yi Aikinsu Duk da Matsaloli

Taron Yanki na 2020 mai jigo, Ku Rika Farin Ciki! daya ne cikin taron Shaidun Jehobah da aka yi a zamaninmu da babu kamarsa. An fassara taron zuwa yaruka fiye da 500 kuma mutane sun kalle shi a gidajensu. Mafassara sun yi aikinsu duk da matsaloli kamar rashin isasshen kayan aiki da rashin isasshen lokaci.

Wata da take fassara yaren Kikuyu a kasar Kenya ta ce: “Da yake an hana mutane shiga da fita daga reshen ofishinmu, mun yi karancin wadanda za su dauki muryoyin mutanen da ke bidiyoyin. Mun magance wannan matsalar ta wurin yin amfani da ’yan’uwa maza da mata a inda suke. Yadda Jehobah ya taimaka mana ta wurin ruhunsa ya burge mu sosai.”

Mafassaran Yaren Kurame na Koriya da mafassaran Yaren Koriya sun fuskanci irin wannan matsalar. Bai yiwu ’yan’uwan da suka saba zuwa su taimaka musu su zo Bethel don a dauki muryoyinsu ba.

Wani daki da aka shirya na dan lokaci, don daukan jawabai da bidiyoyi a Yaren Kurame na Koriya

Don a magance matsalar nan, wasu ’yan’uwa sun shirya wurin daukan sauti a gidajensu. ’Yan’uwan da ke wurin ne suka ba da gudummawar yawancin kayan da aka yi amfani da su. Kari ga haka, da yake an fasa yin manyan taronmu, reshen ofishinmu ta yi amfani da kamarorin da ke Majami’un Manyan Taro wajen daukan bidiyo na yaren kurame.

A Benezuwela kuma, wasu ’yan’uwa sun yi fama da rashin sabis mai karfi. Wasu kuma ba su da isasshen kayan aiki. Amma wadannan mafassara masu basira sun yi amfani da duk abin da suka samu don su yi aikin nan. Alal misali, wasu mafassara sun yi amfani da katifu wajen tare inda na’urar daukan sautin take don muryarsu ta fita da kyau.

Wani mafassarin yaren Zande a birnin Juba da ke kasar Sudan ta Kudu ya ce: “Da na ji cewa za mu dauki sautin duka taron, sai na gaya wa kaina cewa ‘hakan ba zai yiwu ba! Ba za mu iya hada duka bidiyoyin taron da suka fi 90 a cikin wata biyu kawai ba.’ Amma yanzu da muka gama aikin, na tabbata cewa ba abin da zai iya hana Jehobah yin duk abin da yake so. Yana yin abubuwa masu ban mamaki!”​—Matiyu 19:26.

Hakika, Taron Yanki na 2020 mai jigo, Ku Rika Farin Ciki! kyauta ce babba daga wurin Jehobah, “wanda yake so dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.”​—1 Timoti 2:4.