Koma ka ga abin da ke ciki

20 GA JANAIRU, 2020
FILIFIN

Dutse Mai Aman Wuta na Gab da Fashewa a Filifin

Dutse Mai Aman Wuta na Gab da Fashewa a Filifin

A ranar 12 ga Janairu, 2020, dutsen Taal a Batangas, Filifin, ya soma fitar da hayaki da ya tashi sama har kilomita sha hudu. Hakan ya sa hukuma ta gargadi mutane cewa dutsen za ta iya fashewa. Hukuma ta gaya wa dubban mutane da ke zama kusa da dutsen cewa su kaura.

Kawo yanzu, an kaurar da ʼyan’uwa fiye da 500 zuwa Majami’un Mulki da kuma gidajen wasu Shaidun Jehobah. Babu wani cikin ʼyan’uwanmu da ya jikkata. Kwamitin da ke kula da Ofishinmu a kasar ya kafa Kwamitin Agaji don su tanadar da bukatun ʼyan’uwa da suka kaura.

Muna addu’a cewa ʼyan’uwanmu da ke Filifin za su ci gaba da dogara ga Jehobah, wanda “shi ne wurin ɓuyanmu da ƙarfinmu.”​—Zabura 46:​1-3.