Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA FABRAIRU, 2018
AMIRKA

Zaftarewar Laka ta Auku a Kudancin Kalifoniya

Zaftarewar Laka ta Auku a Kudancin Kalifoniya

A ranar 9 ga Janairu, wata mahaukaciyar guguwa ta jawo zaftarewar laka da ta raunana mazaunan kudancin Kalifoniya a Amirka. Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 21 ne suka mutu, darurrukan gidaje kuma sun lalace ko kuma halaka.

Babu Mashaidin Jehobah da ya mutu sanadiyyar bala’in. Amma a birnin Burbank, gidan wani Mashaidi ya lalace, kuma an kaurar da iyalai guda takwas daga birnin Ventura. Babu wata Majami’ar Mulki da bala’in ya shafa.

Masu kula da da’ira da Kwamitin Aikin Agaji da kuma wakilan Kwamitin Gine-Gine, suna tallafa wa masu shela da wannan zaftarewar laka da kuma wutar daji da ta barke kwanan nan ta shafa. Za mu ci gaba da yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu kuma muna da tabbaci cewa Jehobah zai ba su karfin zuciya.—1 Bitrus 5:10.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000