Koma ka ga abin da ke ciki

11 GA SATUMBA, 2017
AMIRKA

Rahoto Game da Mahaukaciyar Guguwar Irma

Rahoto Game da Mahaukaciyar Guguwar Irma

An soma samun rahoto game da yanayin da ’yan’uwanmu da ke Caribbean da kuma kudu maso gabashin Amirka ke ciki bayan mahaukaciyar guguwa mai suna Irma ta yi barna sosai.

Abin takaici, wani dan’uwa da ya tsufa da ke jihar Florida, da kuma wata ’yar’uwa a jihar Georgia sun rasu yayin da ake kokarin fitar da su daga wurin da bala’in ya shafa. Ban da haka ma, a tsibirin Tortola wanda shi ne tsibiri mafi girma a British Virgin Islands, ’yan’uwanmu guda biyu sun ji rauni. A tsibirin Caribbean, fiye da gidaje 40 sun hallaka kuma gidajen akalla ’yan’uwa 40 ne ya halaka. Yanzu da aka samu damar shiga wuraren da bala’in ya shafa ana kokarin tallafa wa ’yan’uwan.

Muna jin tausayi wadanda suka yi rashi da kuma wanda bala’in ya yi musu barna. Za mu ci gaba da dogara ga Jehobah don ya ta’azantar da su ta wurin yin amfani da ikilisiya.​—1 Tasalonikawa 3:7.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000