Koma ka ga abin da ke ciki

14 GA SATUMBA 2017
AMIRKA

Shaidun Jehobah a Amirka Suna Fama Don Barna da Mahaukaciyar Guguwar Harvey Ta Yi

Shaidun Jehobah a Amirka Suna Fama Don Barna da Mahaukaciyar Guguwar Harvey Ta Yi

Rahoto: Abin takaici, an gano cewa wata ‘yar’uwa tsohuwa ta mutu sanaddiyar Mahaukaciyar Guguwar Harvey.

NEW YORK​—A ranar 25 ga Agusta 2017, mahaukaciyar guguwar Harvey ta yi barna sosai a birnin Rockport da ke jihar Texas kuma wannan guguwar ita ce na hudu mafi karfi da ta taba aukuwa. Daga ranar Lahadi, mahaukaciyar guguwar ta ragu zuwa iska mai karfi da ta ci gaba da yin barna sosai a kudu maso gabashin jihar Texas har zuwa ranar Laraba, 30 ga Agusta. Ofishin Shaidun Jehobah a Amirka ta sami rahoto game da yadda bala’in ya shafi ’yan’uwan da ke jihar.

Kimanin Shaidun Jehobah 84,000 ne suke zama a wuraren da mahaukaciyar guguwar Harvey ta shafa. Ba a sami rahoto cewa wani dan’uwa ko ’yar’uwa ta rasa ranta ba. Amma ’yan’uwa tara sun ji rauni kuma biyar suna asibiti. Shaidun Jehobah guda 5,566 ne guguwar ta shafa. Mahaukaciyar guguwar ta halaka gidajen Shaidu guda 475. Kari ga haka, guguwar ta dan lalata gidaje guda 1,182 na Shaidun Jehobah.

Da taimakon masu kula da da’ira a birnin Austin da Dallas da San Antonio, an shirya kayan agajin da za a kai wuraren da guguwar ta shafa. ’Yan’uwa da yawa a biranen nan sun ba da dakuna a gidajensu domin ’yan’uwan da guguwar ta shafa a Houston da kuma gabar tekun Texas su sami masauki. Wasu ’yan’uwan sun ba da gudummawar abinci kusan tan 300 da ruwan sha da kuma wasu abubuwa don mabukata.​—Misalai 3:27; Ibraniyawa 13:​1, 2.

Masu kula da da’ira sun ba da rahoto cewa ’yan’uwa sun soma yin taro da kuma fita wa’azi kamar yadda suka saba. Mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Amirka suna shirin ziyartar wuraren da bala’in ya shafa domin su tallafa da kuma karfafa ’yan’uwa.

David A. Semonian kakakin Shaidun Jehobah, ya ce: “Muna jin tausayin wadanda suke shan wahala sanaddiyar mahaukaciyar guguwar Harvey, kuma muna gode wa wadanda suka ba da kai don tallafa wa ’yan’uwan da bala’in ya shafa. Ban da haka, muna yi wa ’yan’uwanmu musamman ma wadanda bala’in ya shafa addu’a kuma muna karfafa su su ci gaba da dogara ga Jehobah don ya taimaka musu.​—Zabura 55:​8,22; Ishaya 33:2; 40:11.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000