Koma ka ga abin da ke ciki

1 GA SATUMBA, 2020
AMIRKA

Wutar Daji Ta Yi Barna Sosai a Yammacin Amirka

Wutar Daji Ta Yi Barna Sosai a Yammacin Amirka

Inda ya faru

Arewacin Kalifoniya da kuma Oregon

Bala’i

  • Walkiyar da aka yi wajen sau 14,000 da kuma wasu abubuwa ne suka jawo tashiwar wutar dajin. An sami barkewar wutar daji dabam-dabam fiye da 700 da ta hallaka fadin kasa fiye da eka miliyan daya a arewacin Kalifoniya da wasu wurare a Oregon

  • Hayaki da toka sun gurbata iskar da ke yankin sosai. A ranar 21 ga Agusta, an sami labari cewa arewacin Kalifoniya ne ke da iska mafi muni a duk duniya

  • An kuma ba da rahoto cewa a duk tarihin Kalifoniya, biyu daga cikin wutar dajin da suke kan ci har yanzu ne wuta na biyu da kuma na uku mafi girma da aka taba yi

Yadda ya shafi ’yan’uwanmu

  • Masu shela 936 ne suka gudu daga yankin

Abubuwan da aka yi hasararsu

  • Gidajen masu shela 2 sun hallaka

Agaji

  • Wani Kwamitin Aikin Agaji, da masu kula da da’ira da dattawan da suke yankin suna aiki tukuru don su taimaka wa wadanda bala’in ya shafa

’Yan’uwanmu suna godiya sosai don taimakon da suke samu daga kungiyar Jehobah. Wani dan’uwa ya ce: “Ko da me ya faru, ’yan’uwa suna a shirye su zo nan da nan don su taimaka maka. Dukanmu ’yan iyali daya ne.” Kokarin da ake yi don a agaza wa ’yan’uwanmu da bala’i ya fado musu ya tabbatar mana cewa ba abin da ya isa ya “raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana.”​—Romawa 8:39.