Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA YUNI, 2017
SIRI LANKA

Ambaliya da Gocewar Laka Ta Afka a Sri Lanka

Ambaliya da Gocewar Laka Ta Afka a Sri Lanka

Shaidun Jehobah sun yi aiki tukuru wajen taimaka wa ‘yan’uwa da kuma wasu da ambaliya da kuma gocewar laka ta shafa a Sri Lanka. Ambaliya da kuma gocewar laka sun yi barna sosai a kudancin da yammacin Sri Lanka a ranar 26 ga Mayu. Rahotanni sun nuna cewa mutane fiye da 200 ne suka rasa rayukansu kuma mutane fiye da 77,000 ne suka bar gidajensu.

Ofishinmu Shaidun Jehobah da ke Sri Lanka sun kafa kwamitin kula da agaji biyu don su taimaka wa Shaidun Jehobah fiye da 100 da bala’in ya shafa. Agajin sun hada da, abinci da kuma wuraren kwana. Rahotanni sun nuna cewa ba Mashaidin da ya rasa ransa.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun yi amfani da gudummawar da muke samu don fadada aikin wa’azinmu, sun turo nasu agajin daga hedkwatarmu na New York.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Sri Lanka: Nidhu David, +94-11-2930-444