Koma ka ga abin da ke ciki

5 ga AFRILU, 2017
RASHA

Kotun Koli Na Rasha Ta Fara Wata Shaharren Shari’a A Kan Shaidun Jehobah

Kotun Koli Na Rasha Ta Fara Wata Shaharren Shari’a A Kan Shaidun Jehobah

NEW YORK​—A yau, Kotun Koli na Rasha ta fara saurarar daukaka karar da Gwamnatin Rasha ta shigar cewa a rufe Ofishin Shaidun Jehobah a Rasha. Kotun ta ce za ta je hutu, kuma za a ci gaba da saurarar karar a ranar Alhamis, 6 ga Afrailu, 2017 da karfe 2 na rana.

Shaidun ma sun shigar da nasu karar a kan Gwamnatin a ranar 30 ga Maris, 2017, domin zargin da ke musu. A yau dai, bayan sun dawo daga hutu kotun ta yi watsi da karar da Shaidun suka shigar. Kuma Kotun ta ki ta ba wa kwararu dama domin yin mahawa a kan zargin da Gwamnati suka yi. Ban da haka, ta hana wadanda suka ga yadda aka kaga wannan zargin a kan kungiyar adinin Shaidun Jehobah, ba da bayani.

Wannan shahararren karar ta jawo hankulan ‘yan jeridu daga fadin duniya, har da wani talifi daga Time magazine da aka saka a intane a ranar 4 ga Afrilu (“Kotun Koli na Rasha Tana So Ta Hana Shaidun Jehobah Yin Ibadarsu”) wata talifi a bangon mujallar The New York Times kuma ta ce (“Rasha na Barazanar Kafa Dokar Hana Wata Adinin Kirista, Wanda Ba Su Son Zub Da Jini Cewa Su ‘Masu tsatauran Ra’ayi Ne’”) a ranar 5 ga Afrilu.

Kakakin Shaidun Jehobah a hedkwatarsu a New York ya ce: “Muna fatan cewa Kotun Koli na Rasha za ta daukaka ‘yancin ‘yan’uwanmu da ke Rasha don su ci gaba da ibadarsu cikin salama,” ya dada cewa “Milliyoyin mutane a fadin duniya sun zuba ido su ga sakamakon yadda karar za ta zama kuma ko Rasha za ta kare ‘yan kasanta masu kiyaye doka, wato Shaidun Jehobah.”

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-812-702-2691