Koma ka ga abin da ke ciki

6 GA AFRILU, 2017
RASHA

Kotun Rasha Ya Ci gaba da Saurarar Karar da Aka Shigar Game da Shaidun Jehobah

Kotun Rasha Ya Ci gaba da Saurarar Karar da Aka Shigar Game da Shaidun Jehobah

A rana ta biyu, Kotun Kolin Rasha ya ci gaba da sauraron karar da Ma’aikatan Shari’a ta shigar don neman damar rufe Ofishin Shaidun Jehobah da ke Rasha. A karshe, kotun ya sanar cewa za a je hutu sai karfe 10 na safe a ranar Jumma’a, 7 ga Afrilu, 2017, kafin ya ci gaba da sauraron karar.

Kakakin Shaidun Jehobah da ke hedkwatarmu a New York mai suna David A. Semonian ya bayyana cewa: “Bincike na yau ya nuna cewa Ma’aikatan Shari’a na Rasha ba ta da wata hujjar da ta goyi bayan zargin da ta ke yi wa kungiyarmu.” Ya ce, “Amma mun san cewa kamar yadda Ma’aikatar Shari’a ta fada yau, idan aka hana ayyukan Shaidun Jehobah a Rasha, za a rika kama su, ko da sun taru don yin addu’a ne kawai. Muna fatan cewa Kotun Koli zai yi adalci a wannan shari’ar don a daina taka hakkinmu na bin addini.”

Inda Aka Samo Labarin:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Russia: Yaroslav Sivulskiy, +7-812-702-2691