Koma ka ga abin da ke ciki

30 GA MARIS, 2017
LABARAN DUNIYA

Shaidun Jehobah Suna Shirin Yin Wani Taro Mai Muhimmanci a 2017

Shaidun Jehobah Suna Shirin Yin Wani Taro Mai Muhimmanci a 2017

NEW YORK​—⁠Shaidun Jehobah za su gayyaci jama’a halartan taro masu muhimmanci da za su yi a shekara ta 2017.

A ranar Talata, 11 ga Afrilu, 2017, Shaidun Jehobah a dukan fadin duniya za su marabci jama’a zuwa Jibin Maraice na Ubangiji wanda ake kira Taron Tuna da Mutuwar Yesu da suke yi kowace shekara. Za su soma yin kamfen don gayyatar mutane daga ranar Asabar 18 ga Maris, zuwa 11 ga Afrilu, 2017. Suna son su yi wannan kamfen ne don su gayyaci mutane da yawa. Saboda haka, suna ba da katin gayyata da aka rubuta adireshin wurin da za a yi taron da kuma wasu bayane. Wannan taron ne mafi muhimmanci a taron da suke yi a shekara.

Bayan an kammala taron, Shaidun za su gayyaci jama’a don su zo su saurari jawabi daga Littafi Mai Tsarki da za a ba da a cikin minti 30 mai jigo “Ku Biɗi Zaman Lafiya a Duniyar da ke Cike da Mugunta.” Wannan jigo ne za su tattauna a taro don jama’a a karshen makon 15 da 16 ga Afrilu a kusan duka Majami’un Mulkin Shaidun Jehobah a fadin duniya.

Daga 19 ga Mayu, 2017, Shaidun Jehobah za su soma halartan taronsu na yanki da ake yi kwana uku kuma jigon taron shi ne “Kar Ka Gaji!” Za a soma wannan taron ne a Amirka kuma a ci gaba da yi a wasu kasashe har farawa shekara ta 2018. A kowane taron yanki da Shaidun za su yi suna yin kamfen na wata uku don su gayyaci jama’a zuwa taron.

Wadannan taron har ma da wadanda suke yi a Majami’unsu, kyauta ne ba a karban kudi. Ana gayyatar kafofin yada labarai don su zo su dauki wannan taro da za a yi a yankinsu amma su tuntubi ofishin Shaidun Jehobah da ke yankin don su tallafa musu.

Media Contact:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000