Koma ka ga abin da ke ciki

25 GA FABRAIRU, 2016
LABARAN DUNIYA

Shaidun Jehobah Suna Gayyatar Mutane Su Halarci Taron Tuna da Mutuwar Yesu

Shaidun Jehobah Suna Gayyatar Mutane Su Halarci Taron Tuna da Mutuwar Yesu

Za a ba da jawabi daga Littafi Mai Tsarki a wannan taron Tuna da Mutuwar Yesu.

A RANAR Asabar, 27 ga Fabrairu, Shaidun Jehobah za su soma kamfen na gayyatar mutane su halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu da za a yi a ranar 23 ga watan Maris. Suna daukan wannan taron da suke yi a kowace shekara da muhimmanci sosai. Wani kakakin Shaidun Jehobah mai suna David A. Semonian da ke hedkwatarsu a Amirka ya ce: “A wannan taron, za a ba da jawabin da zai bayyana dalilin da ya sa mutuwar da Yesu ya yi kusan shekaru dubu biyu da suka shige take da muhimmanci sosai a zamaninmu da kuma yadda ta sa mutane su kasance da bege. Muna so mutane da yawa su amfana daga wannan jawabi na taron Tuna da Mutuwar Yesu.”

A lokacin wannan kamfen, Shaidun Jehobah miliyan takwas a dukan duniya za su ziyarci makwabtansu don su gayyace su zuwa wannan taron. A shekarar da ta shige, mutane kusan miliyan 20 ne suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu.

Ku Tuntubi:

David A. Semonian, Office of Public Information, tel. +1 718 560 5000