Koma ka ga abin da ke ciki

17 GA MAYU, 2017
AMIRKA

Shaidun Jehobah Sun Sayar da Wani Ginin da Ke 107 Columbia Heights, Brooklyn

Shaidun Jehobah Sun Sayar da Wani Ginin da Ke 107 Columbia Heights, Brooklyn

NEW YORK​—A ranar 9 ga Mayu 2017, Shaidun Jehobah sun amince su sayar wa wani kwamfani mai suna Clipper Realty gininsu na 107 Columbia Heights da ke Brooklyn Heights New York. Shaidun Jehobah da suke aiki a hedkwatarsu ne ke zama a ciki tun shekara ta 1960.

Ginin gida ne mai hawa 11 kuma yana da fadin kafa 154,058. Yana da lambu da kuma kagaggen marmaro a farfajiyarsa, mutum yana iya ganin gadar Brooklyn, da kuma Lower Manhattan daga wurin.

Kakakin Shaidun Jehobah da ke sabon hedkwatarsu a Warwick, New York mai suna David A. Semonian ya ce: “Muna jin daɗin ganin makwabtanmu, musamman ma ma’aurata da ba su dade da aure ba suna sha’awar kagaggen marmaronmu da lambunmu a 107 Columbia Heights yayinda suke shigewa a gaban wurin. Hakika, mun ji daɗin amfani da wannan ginin fiye da shekara 50 kuma yana cikin gidajen da sun isa a zo a gani a unguwar Brooklyn Heights.”

Yadda lambun da ƙagaggen marmaron suke a 107 Columbia Heights.

Inda Aka Samo Labarin:

David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000