Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA MAYU, 2017
HAITI

An Kusan Kammala Rarraba Kayan Agaji don Guguwar Matthew a Haiti

An Kusan Kammala Rarraba Kayan Agaji don Guguwar Matthew a Haiti

Kwamitin tara kayan agaji suna sa rufi a kan wannan gida.

PORT-AU-PRINCE, Haiti​—Tun shekara ta 2010, ba a taba yin guguwa a Haiti da ta yi barna kamar na mahaukaciyar guguwar Matthew da ta auku a ranar 4 ga Oktoba 2016 ba. An sami labari a ranar 24 ga Oktoba 2016, daga Dakin Watsa Labaru na jw.org cewa Shaidun Jehobah sun tura kayan agaji kamar abinci da magunguna da kuma kayan kwanciya. Bayan da Shaidun sun yi la’akari da barnar da guguwar ta yi, sai suka sake tsara ma’aikatan da za su kai kayan agaji a ranar 1 ga Janairu 2017, sun kafa kwamitin tara kayan agaji guda uku don su ja-goranci rukunin masu gini guda 14 da suka riga suka soma aiki a kan gidaje 203 da suka lalace. Ana so a kammala wannan aikin a watan Yuni 2017.

Wani wakilin Shaidun Jehobah a Port-au-Prince mai suna Daniel Lainé ya ce: “Manufar wannan aikin shi ne don mu gina wa ‘yan’uwanmu waɗanda guguwar nan ta lalatar da gidajensu.” Cim ma burin nan ba abu mai sauki ba ne. Ɗan’uwa Lainé ya ce “zai zama mana da wuya mu yi aikinmu yadda ya kamata “ domin hanyoyi da kum wayar tarho da suka lalace a sakamakon guguwar An rigaya an kammala aiki a gidaje 96, kuma ana nan ana kan aiki a kan gidaje 30 ranar 20 ga Afrilu.

Smith Mathurin, mataimakin shugaban Parliament for the hard-hit communes of Paillant and Petite Rivière de Nippesb.

Ma’ikatan gwamnatin da ke yankin sun yaba wa aikin da Shaidun Jehobah suka yi. Wani shugaban ma’aikata da ake kira Parliament for the hard-hit communes of Paillant and Petite Rivière de Nippes mai suna Daniel Lainé ya ce: “Ko da shi keke ainihin aikin da Shaidun Jehobah suke yi shi ne yin wa’azi, amma kuma sun ba da kansu don su taimaka wa waɗanda ke cikin bukata.” Ya dada da cewa: “Ina matukar godiya ga taimakon da Shaidun Jehobah suka yi bayan wannan aukuwar. Ana bukatar taimako, kuma ba ku je kun zauna cikin cocinku shiru ba amma kun yi abin da ake bukata.”

Ana nuna wa wani wakilin Shaidun Jehobah na Haiti zanen sabon rufin wani gida.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun yi amfani da gudummawar da ake bayarwa wajen tanadar da kayan agaji daga hedkwatarsu a Warwick, New York.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

Haiti: Daniel Lainé, +509-2813-1560