Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Mene ne Ake Nufi da Zuwan Yesu?

Mene ne Ake Nufi da Zuwan Yesu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

An rubuta annabce-annabce da dama a cikin Nassosi game da lokacin da Yesu zai zo ya hukunta mutane. * Alal misali, Matta 25:31-33 sun ce:

“Sa’an da Dan mutum [Yesu Kristi] za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awaki: kuma za ya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu.”

Wannan lokacin shari’a zai zama lokacin “kunci mai girma” wanda bai taba faruwa a duniya ba. Za a sha wannan kunci har zuwa yakin Armageddon. (Matta 24:21; Ru’ya ta Yohanna 16:16) Magabtan Kristi, wato wadanda Yesu ya ce da su awaki a kwatancinsa za su “sha hukuncin madawwamiyar halaka.” (2 Tasalonikawa 1:9, Littafi Mai Tsarki; Ru’ya ta Yohanna 19:11, 15) Amma, bayinsa masu aminci da aka ce da su tumaki, za su sami “rai na har abada.”Matta 25:46.

Yaushe ne Kristi zai zo?

Yesu ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani.” (Matta 24:36, 42; 25:13) Amma ya ba da jerin ‘alamu’ da za su nuna cewa lokacin zuwansa ya kusa.—Matta 24:3, 7-14; Luka 21:10, 11.

Kristi zai zo da jikin ruhu ne ko na zahiri?

An ta da Yesu daga mutuwa da jikin ruhu, saboda haka zai zo a matsayin ruhu ne, ba a matsayin dan Adam ba. (1 Korintiyawa 15:45; 1 Bitrus 3:18) Wannan dalilin ne ya sa kwana daya kafin mutuwar Yesu, ya gaya wa manzanninsa cewa: “Saura dan lokaci kadan duniya ba za ta kara ganina ba.”—Yohanna 14:19, LMT.

Wasu ra’ayoyi game da zuwan Kristi da ba daidai ba

Ra’ayi: Yesu zai bayyana a zahiri domin Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su gan shi yana “zuwa kan gajimare.”—Matta 24:30.

Gaskiyar al’amarin: Sau da yawa idan aka yi magana game da gajimare a cikin Littafi Mai Tsarki, ana nufin abin da ba a gani. (Levitikus 16:2; Littafin Lissafi 11:25; Kubawar Shari’a 33:26) Alal misali, Allah ya gaya wa Musa cewa: “Ina zuwa gare ka cikin bakin hadari,” ko kuma gajimare. (Fitowa 19:9) Musa bai gan Allah ido-da-ido ko kuma a zahiri ba. Hakazalika, idan aka ce Kristi yana “zuwa kan gajimare” ana nufin mutane za su gane cewa ya zo, ko da yake ba za su gan shi ido-da-ido ba.

Ra’ayi: Furucin nan “kowane ido kuma za ya gan shi” a Ru’ya ta Yohanna 1:7, yana da ma’ana ta zahiri.

Gaskiyar al’amarin: A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmomin Helenanci da akan yi amfani da su domin “ido” da kuma “gani” suna iya nufin gane wani abu, ba ganin abu a zahiri ba. * (Matta 13:15; Luka 19:42; Romawa 15:21; Afisawa 1:18) Littafi Mai Tsarki ya ce bayan an ta da Yesu daga mutuwa, mazauninsa na “cikin haske wanda ba shi kusantuwa ... ba kuwa mai-ikon ganinsa.” (1 Timotawus 6:16) Saboda haka, furucin nan “kowane ido kuma za ya gan shi,” yana nufin mutane za su gane cewa Yesu ne zai zartar da hukunci a kansu.—Matta 24:30.

^ sakin layi na 3 Ko da yake mutane da yawa suna amfani da furucin nan “zuwa na biyu” sa’ad da suke zancen zuwan Kristi, babu wannan furucin a cikin Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 14 Ka duba The New Thayer’s Greek-English Lexicon of the New Testament (1981), shafuffuka na 451 da 470.