Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Zunubin da Ba A Gafartawa?

Mene ne Zunubin da Ba A Gafartawa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Zunubin da ba a gafartawa yana nufin abubuwan da mutum ya yi da kuma hali da zai sa Allah ba zai gafarta masa ba. Ta yaya hakan zai iya faruwa?

 Allah yana gafarta wa wadanda suka tuba daga zunubansu kuma suka ba da gaskiya ga Yesu Kristi ta wajen bin ka’idodin Allah. (Ayyukan Manzanni 3:19, 20) Amma mutum zai iya ci gaba da yin zunubi har zuciyarsa ta yi tauri kuma ya ci gaba da yin mugayen ayyukan da kuma halayen banza. Littafi Mai Tsarki ya ce irin wannan mutum yana da ‘muguwar zuciya’ da ta “taurare ta wurin rikicin zunubi.” (Ibraniyawa 3:12, 13) Kamar yumbun da ya sha wutar tanderu da ba za a iya mulmulawa ba, zuciyar irin wannan mutum ya gama lalacewa don ya nace a yin abubuwan da Allah ya haramta kuma ba zai taba canja halinsa ba. (Ishaya 45:9) Irin wannan yanayin zai sa Allah ba zai taba gafarta masa zunubansa ba.—Ibraniyawa 10:26, 27.

 Wasu shugabannin addinin Yahudawa a zamanin Yesu sun yi zunubin da ba za a gafarta musu ba. Sun san cewa Yesu yana mu’ujizai da taimakon ruhu mai tsarki na Allah. Amma saboda yawan muguntarsu, sun ce Shaiɗan ne ya ba shi ikon yin mu’ujizai.—Markus 3:22, 28-30.

Wasu zunuban da za a iya gafartawa

  •  Ya yi abubuwan da Allah ya haramta cikin rashin sani. Manzo Bulus ya taba yin abubuwan da Allah ya haramta amma daga baya ya ce: “Na sami jinƙai, domin da rashin sani na yi shi cikin rashin bangaskiya.”—1 Timotawus 1:13.

  •  Zina. Littafi Mai Tsarki ya ambaci wasu mutane da suka yi zina a dā amma daga baya suka tuba kuma suka canja halayensu. Saboda haka, Allah ya gafarta musu zunubansu.—1 Korintiyawa 6:9-11.

“Shin na aikata zunubin da ba za a taba gafartawa ba?”

 Idan ka tsani zunuban da ka yi a dā kuma kana so ka canja halinka, ba ka yi zunubin da ba za a gafartawa ba. Allah zai gafarta maka ko da a wani lokaci kana sake yin wadannan abubuwan, muddin ba ka kasance da taurin zuciya a gare shi ba.—Misalai 24:16.

 Wasu mutane sun dauka cewa watakila sun yi zunubin da ba za a gafarta musu ba don yadda zuciyar take damunsu. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce zuciyarmu ta fi kome rikici. (Irmiya 17:9) Allah bai ba mu izinin yin hukunci ba. Saboda haka, kada mu hukunta kanmu. (Romawa 14:4, 12) Allah zai iya gafarta mana ko da zuciyarmu tana damunmu.—1 Yohanna 3:19, 20.

Yahuda Iskariyoti ya yi zunubin da ba a gafartawa ne?

 Hakika. Kwadayi ya sa shi satan kudin da aka kebe don bisharar Mulki. Ya nuna kamar ya damu da talakawa ne, amma alhali bai damu da su ba. Ya yi hakan ne kawai don ya sami damar kara sata kudi. (Yohanna 12:4-8) Yahuda ya ci gaba da yin zunubi har lamirinsa ya daina damunsa, kuma hakan ya sa ya karbi azurfa talatin don ya ci amanar Yesu. Yesu ya san cewa Yahuda ba zai taba tuba daga abin da ya yi ba. Shi ya sa ya kira shi “ɗan lalacewa.” (Yohanna 17:12) Hakan yana nufin cewa ba za a ta da Yahuda daga mutuwa ba.—Markus 14:21.

 Yahuda bai tuba da gaske daga zunubansa ba. Ya yi ikirari ga shugabannin addini da ya hada baki da su, ba ga Allah ba.—Matta 27:3-5; 2 Korintiyawa 7:10.