Koma ka ga abin da ke ciki

Idan Zuciyata Tana Damu Na, Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min?

Idan Zuciyata Tana Damu Na, Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E. Littafi Mai Tsarki zai iya gaya mana abin da za mu yi don zuciyarmu ta daina damun mu. (Zabura 32:​1-5) Idan mun yi abin da bai dace ba kuma muka tuba, Allah zai gafarta mana kuma ya taimake mu. (Zabura 86:5) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutum zai iya amfana idan zuciyarsa ta dame shi. Hakan zai iya taimaka wa mutum ya daina yin abin da ba kyau kuma ya yi kokari ya guji maimaita kuskuren da ya yi. (Zabura 51:17; Karin Magana 14:9) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawara cewa kar mu bar zuciyarmu ta yi ta damun mu har mu ji kamar ba mu cancanci samun alherin Allah ba. Irin ra’ayin nan zai iya sa ‘bakin ciki ya sha karfinmu.’​—2 Korintiyawa 2:7.

 Me da me za su iya sa zuciyar mutum ta dinga damun sa?

 Akwai abubuwa da dama da za su iya sa zuciyarmu ta dame mu. Hakan zai iya faruwa idan mun bata ran wani da muke kauna, ko mun kasa yin abin da ya kamata mu yi. A wasu lokuta, zuciyarmu za ta iya damun mu ko da ba mu yi laifi ba. Alal misali, idan muka sa ran yin wani abin da ya fi karfinmu kuma muka gagara yi, zuciyarmu za ta iya damun mu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawara cewa kada mu sa hannu a abin da ya fi karfinmu.​—Mai-Wa’azi 7:16.

 Me zan yi don zuciyata ta daina damu na?

 Maimakon ka dauka cewa taka ta kare, ka dauki matakin daidaita yanayin. Me za ka yi?

  •   Ka yarda cewa ka yi kuskure. Ka yi addu’a, ka roki Jehobah a ya gafarta maka. (Zabura 38:18; Luka 11:4) Allah zai gafarta maka idan ka tuba, ka yi da-na-sani, kuma ka kokarta kada ka sake yin kuskuren. (2 Tarihi 33:13; Zabura 34:18) Allah yana iya ganin zuciyar dan Adam, abin da ba wanda zai iya yi. Idan Allah ya ga cewa muna kokari don mu daina yin abu marar kyau, “shi mai aminci ne, mai gaskiya kuma, zai kuma gafarta mana zunubanmu.”​—1 Yohanna 1:9; Karin Magana 28:13.

     Idan ka yi wa wani ne laifi, zai dace ka yarda cewa ka yi kuskure kuma ka ba shi hakuri. Hakan bai da sauki domin kana bukatar karfin zuciya da kuma tawali’u. Idan ka ba wa mutumin hakuri, za ka amfana a hanyoyi biyu: Za ka sami kwanciyar hankali kuma dangantakarku za ta gyaru.​—Matiyu 3:8; 5:​23, 24.

  •   Ka yi tunani a kan nassosin da suka nuna cewa Allah mai jin kai ne. Alal misali, ka karanta 1 Yohanna 3:​19, 20. A wurin Littafi Mai Tsarki ya ce zuciyarmu za ta iya “nuna mana muna da laifi,” wato za mu iya dauka cewa ba mu da amfani kuma ba mu cancanci Allah ya nuna mana kauna ba. Amma nassin ya ce “Allah ya fi zuciyarmu.” Allah fi zuciyarmu domin ya san ainihin yadda muke ji da kuma kasawarmu. Ya kuma san cewa mu masu zunubi ne, don haka, yana da sauki mu yi abin da bai da kyau. b (Zabura 51:5) Saboda haka, Allah ba ya watsi da wadanda suka tuba.​—Zabura 32:5.

  •   Kada ka yi ta tunanin kuskuren da ka yi. Littafi Mai Tsarki na dauke da labaran maza da matan da suka yi wani abin da bai dace ba amma daga baya sun tuba kuma sun daina. Mutum daya daga cikin su shi ne Shawulu mutumin Tarsus, wanda daga baya aka kira shi manzo Bulus. A lokacin da shi Bafarisi ne, ya wulakanta mabiyan Yesu sosai. (Ayyukan Manzanni 8:3; 9:​1, 2, 11) Amma da ya gano cewa Allah da kuma Almasihu ne yake gāba da su, sai ya tuba kuma ya canja halinsa, har ya zama Kiristan da ya kafa misali mai kyau. Ko da yake Bulus ya yi nadama, bai bar hakan ya yi ta damun sa ba. Bulus ya san cewa Allah ya nuna masa jin kai. Hakan ya sa ya yi wa’azi da kwazo sosai kuma ya mai da hankali ga samun rai na har abada.​—Filibiyawa 3:​13, 14.

 Nassosi game da gafara da kuma zuciya mai damun mutum

 Zabura 51:17: “Zuciya mai tuba ba za ka ki ba, ya Allah.”

 Ma’ana: Allah ba zai ki ka don kuskuren da ka yi ba idan ka yi nadama kuma ka roke shi gafara. Zai yi maka jin kai.

 Karin Magana 28:13: “Duk wanda ya rufe zunubansa, ba zai ci gaba ba, amma wanda ya furta ya kuma ki su, zai sami jinkai.”

 Ma’ana: Idan muka amince cewa mun yi zunubi kuma muka daina zunubin, Allah zai gafarta mana.

 Irmiya 31:34: “Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan sāke tunawa da zunubansu ba.”

 Ma’ana: Da zarar Allah ya gafarta mana, ba zai sake tuna mana zunubin da muka yi ba. Idan ya yafe, ya yafe ke nan.

a Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah.​—Fitowa 6:3.

b Mun gāji ajizanci daga mutum na farko, wato Adamu. Don haka, haifan mu ake yi da zunubi. Adamu ya bi matarsa ya yi wa Allah rashin biyayya kuma sun zama ajizai. Haka ma yaran da suka haifa sun zama ajizai.​—Farawa 3:​17-19; Romawa 5:12.