Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Su Waye Za Su Je Sama?

Su Waye Za Su Je Sama?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Allah ya zabi Kiristoci kadan daga cikin masu aminci don su je sama. (1 Bitrus 1:3, 4) Wadannan Kiristocin suna bukatar su ci gaba da rike amincinsu kuma su ci gaba da kasancewa da dabi’u masu kyau domin su iya samun wannan ladan.—Afisawa 5:5; Filibiyawa 3:12-14.

Wane aiki ne wadanda za su je sama za su yi?

Za su hada hannu da Yesu su yi sarauta kuma su yi aikin firistoci na shekaru 1,000. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 20:6) Ana iya ce da su “sabbabin sammai” ko kuma gwamnati ta sama, wadda za ta yi sarauta bisa “sabuwar duniya” ko talakawan Mulkin Allah da za su kasance a duniya. Su ne za su maido da yanayi mai kyau da Allah ya nufa tun asali wa duniyar nan.—Ishaya 65:17; 2 Bitrus 3:13.

Mutane nawa ne za su je sama?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za a ta da mutane 144,000 zuwa sama. (Ru’ya ta Yohanna 7:4) A cikin wahayin da ke Ru’ya ta Yohanna 14:1-3, manzo Yohanna ya ga “Dan Ragon nan tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu dari da dubu arba’in da hudu tare da shi.” A cikin wannan wahayin, “Dan Ragon” yana nufin Yesu, wanda aka ta da shi daga mutuwa. (Yohanna 1:29; 1 Bitrus 1:19) “Dutsen Sihiyona” kuma yana nufin matsayin daukaka da Yesu da kuma 144,000 da za su yi sarauta tare da shi a sama suka samu.—Zabura 2:6; Ibraniyawa 12:22.

An ce da wadannan “kirayayyu, zababu” da za su yi sarauta tare da Kristi cikin mulkinsa, “karamin garke.” (Ru’ya ta Yohanna 17:14; Luka 12:32) Hakan yana nuna cewa ba su da yawa idan aka hada yawansu da sauran tumakin Yesu gaba daya.Yohanna 10:16.

Ra’ayin da bai dace ba game da wadanda za su je sama

Karya: Dukan masu adalci za su je sama.

Gaskiya: Allah ya yi alkawari cewa yawancin masu adalci za su zauna a duniya har abada.—Zabura 37:11, 29, 34.

  • Yesu ya ce: “Ba wanda ya taba hawa [zuwa] cikin Sama.” (Yohanna 3:13) Ta hakan Yesu ya nuna cewa mutane masu adalci da suka mutu kafin shi, kamar su Ibrahim da Musa da Ayuba da kuma Dauda ba su je sama ba. (Ayyukan Manzanni 2:29, 34) Maimakon haka, sun sa rai cewa za a ta da su su zauna a duniya har abada.—Ayuba 14:13-15.

  • Ana kiran tashi daga mutuwa zuwa rayuwa cikin sama “tashi na fari.” (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Hakan yana nufin cewa ban da wadannan, za a ta da wasu matattu dabam. Wato, za a tashe su su zauna a duniya.

  • Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa a cikin Mulkin Allah, “mutuwa ... ba za ta kara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Hakika wannan alkawarin ya shafi duniya ne domin ba a taba mutuwa a sama ba.

Karya: Mutum zai iya zaban inda yake so ya zauna, ko a sama ko a duniya.

Gaskiya: Allah ne yake zaban Kiristoci masu aminci da za su sami “ladan kiran nan zuwa sama,” wato, begen rayuwa a sama. (Filibiyawa 3:14, Littafi Mai Tsarki) Ko da mutum yana da burin zuwa sama, hakan ba ya nufin cewa Allah zai zabe shi.Matta 20:20-23.

Karya: Ladan zama a cikin aljanna a duniya bai kai ladan zuwa sama ba domin wadanda ba su cancanci su je sama ba ne ake barin su a duniya.

Gaskiya: Allah ya kira wadanda za su zauna a duniya, “mutanena” da “zababuna” da kuma “masu albarka na Ubangiji.” (Ishaya 65:21-23) Za su sami damar cika asalin nufin Allah ga ’yan Adam, wato, na zama har abada a duniya a cikin koshin lafiya.Farawa 1:28; Zabura 115:16; Ishaya 45:18.

Karya: Lambar nan 144,000, da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna kwatanci ne kawai, ba lamba ta zahiri ba ce.

Gaskiya: Ko da yake akwai lambobin da aka yi amfani da su a alamance a littafin Ru’ya ta Yohanna, wasu lambobin na zahiri ne. Alal misali, littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi maganar “sunaye goma sha biyu na manzanni [goma sha biyu] na Dan rago.” (Ru’ya ta Yohanna 21:14) Ga dalilan da suka sa muka yarda cewa lambar nan 144,000 lamba ce ta zahiri.

Littafin Ru’ya ta Yohanna 7:4 ta ce yawan “wadanda aka hatimce su [wato, wadanda suke da tabbaci cewa za su je sama], dubu dari da dubu arba’in da hudu” ne. A ayoyin da ke biye da ayar da aka ambata a sama, an kwatanta wasu dabam kuma a matsayin “taro mai girma, wanda ba mai iya kirgawa.” Su ma za su sami ladan rai na har abada. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Da a ce an yi amfani da lambar nan, 144,000 a alamance ne kawai, da kwatanta bambanci tsakanin rukunin biyu ba zai kasance da amfani ba. *

Kari ga hakan, an kwatanta wadannan mutane 144,000 a matsayin wadanda aka fanshe su “daga cikin mutane, su zama nunan fari.” (Ru’ya ta Yohanna 14:4) Furucin nan “nunan fari” ya nuna cewa su kadan ne. Kuma su ne wadanda za su yi mulki tare da Yesu a sama bisa taro mai girma da za su zauna a duniyar nan.—Ru’ya ta Yohanna 5:10.

^ sakin layi na 21 Wani Farfesa mai suna Robert L. Thomas ya ce: “Lambar nan 144,000 da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:4 ya sha bambam da wadda aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9 domin wadda ke 7:9 ba ta da iyaka. Da a ce an yi amfani da lambar a alamance ne kawai, da duka lambobin da ke Ru’ya ta Yohanna za su zama na alama ne kawai.”Revelation 1-7: An Exegetical Commentary, shafi na 474.