Amsar Littafi Mai Tsarki

Wajibi ne mu yi addu’a ga Allah cikin sunan Yesu domin ta hakan ne kadai Allah ya ce mu yi masa Addu’a. Yesu ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Yesu ya kuma gaya wa manzanninsa masu aminci: “Hakika, hakika, ina ce muku, Idan kun roki komi ga Uba, za ya ba ku a cikin sunana.”—Yohanna 16:23.

Karin dalilai na yin addu’a a cikin sunan Yesu

  • Muna daraja Yesu da Ubansa, Jehobah Allah.—Filibiyawa 2:9-11.

  • Muna nuna godiya ga Allah saboda tanadin mutuwar Yesu don cetonmu.—Matta 20:28; Ayyukan Manzanni 4:12.

  • Muna nuna mun fahimci matsayin Yesu na Matsakaici tsakanin mutane da Allah.—Ibraniyawa 7:25.

  • Muna nuna mun daraja aikin da Yesu yake yi na Babban Firist da zai taimake mu mu kasance da tsayawa mai kyau wajen Allah.—Ibraniyawa 4:14-16.