Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Yesu Ya Yi Aure Ne? Yana da ’Yan’uwa Kuwa?

Yesu Ya Yi Aure Ne? Yana da ’Yan’uwa Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya bayyana a fili cewa Yesu bai yi aure ba. * Bincika wadannan furuci na gaba.

  1. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da iyalin Yesu ya hada ne da mata da suke wa’azi tare da shi kuma da suke wajen sa’ad da aka kashe shi, amma bai taba ambata cewa yana da mata ba. (Matta 12:46, 47; Markus 3:31, 32; 15:40; Luka 8:2, 3, 19, 20; Yohanna 19:25) Takamaiman dalili da ya sa Littafi Mai Tsarki bai ambata wannan ba shi ne cewa bai taba yin aure ba.

  2. Yesu ya gaya wa wadanda suka ki su yi aure don kwazon da suke da shi na yin aikin bisharar Allah cewa: “Wanda ya ke da iko shi karɓi wannan [wato, rashin aure] shi karɓa.” (Matta 19:10-12) Ya nuna misali mai kyau wa wadanda suke son su kebe kansu sosai ga yin ibada ga Allah.—Yohanna 13:15; 1 Korintiyawa 7:32-38.

  3. Yesu ya shirya yadda za a ci gaba da kula da uwarsa kafin ya mutu. (Yohanna 19:25-27) Ko da ma Yesu ya yi aure kuma yana da iyali da zai shirya yadda iyalinsa za su sami biyan bukata.

  4. Littafi Mai Tsarki ya ambata Yesu misali wa mazaje, amma bai ce ga yadda ya yi sha’ani da matarsa ba. Maimako ya ce: “Ku mazaje, ku kaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya kaunaci ikilisiya, ya ba da kansa domin ta.” (Afisawa 5:25) Da Yesu ya yi aure sa’ad da yake duniya, lallai da an yi amfani da misalinsa mafi kyau cikin wannan ayar.

Yesu yana da kanne kuwa?

Yesu yana da kannensa shida. Mazan su ne Yakub, Yusufu, Siman da Yahuda, da kuma mata biyu. (Matta 13:54-56; Markus 6:3) Wadannan yara, yaran uwar Yesu ce da mijinta Yusufu. (Matta 1:25) Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ‘dan farin’ Maryamu ce, wato, yana nufin tana da wasu yara kuma ke nan.Luka 2:7.

Ra’ayi marar kyau game da kannen Yesu

Wasu sun ce yadda aka yi amfani da furuci “’yan’uwa” ma’anarsa dabam ne cikin batun nan domin su ba da goyon baya ga koyarwar cewa Maryamu budurwa ce. Alal misali, wasu suna jin cewa ’yan’uwan Yesu ’ya’yan Yusufu ne ta wajen wata matarsa ta fari. Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ya gaji ikon sarauta da aka yi alkawarinsa wa Dawuda ne. (2 Samaila 7:12, 13; Luka 1:32) Da a ce Yusufu yana da ’ya’ya maza da suka girme Yesu ne da daya cikinsu zai zama magajin Yusufu.

Anya wannan furucin yana zance game da almajiran ko kuma ’yan’uwan Yesu ne? Wannan ya saba wa abin da Nassi ya ce, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “’Yan’uwansa ba su ba da gaskiya gare shi ba” a lokacin. (Yohanna 7:5) Littafi Mai Tsarki ya bambanta kannen Yesu sarai daga almajiransa.Yohanna 2:12.

A wani sassa, kannen Yesu, ’yan ubansa ne. Nassosin Helenanci sun yi amfani da kalmomi dabam dabam wa “dan’uwa” “dangi” da kuma “dan uba.” (Luka 21:16; Kolosiyawa 4:10) Daliban Littafi Mai Tsarki sun yarda da cewa ’yan’uwan Yesu maza da mata ƙannensa ne. Alal misali, kundin Expositor’s Bible Commentary ya ce: “Yadda za a fi fahimta batun ‘’yan’uwa’ . . . shi ne cewa ’ya’yan Maryamu ne da Yusufu.” *

^ sakin layi na 3 Littafi Mai Tsarki ya ce Kristi ango ne, amma mahallin ya bayyana cewa furucin nan na alama ne.—Yohanna 3:28, 29; 2 Korintiyawa 11:2.

^ sakin layi na 13 Duba The Gospel According to St. Mark, fitowa ta biyun, na Vincent Taylor, shafi na 249, da kuma A Marginal Jew—Rethinking the Historical Jesus, na John P. Meier, Littafi na 1, shafuffuka 331-332.