Koma ka ga abin da ke ciki

Yesu Allah Maɗaukaki ne?

Yesu Allah Maɗaukaki ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

’Yan adawa sun zargi Yesu cewa ya ce shi da Allah ɗaya ne. (Yohanna 5:18; 10:30-33) Amma dai, Yesu bai taɓa ce shi daidai ne da Allah Maɗaukaki ba. Ya ce: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.

Mabiyan Yesu na farko ba su ce shi daidai ne da Allah Maɗaukaki ba. Alal misali, manzo Bulus ya rubuta bayan da aka ta da Yesu daga matattu, cewa Allah “ya ba [Yesu] mafificiyar ɗaukaka.” Hakika, Bulus bai amince cewa Yesu Allah ne Maɗaukaki ba. Idan ba haka ba, ta yaya Allah zai ɗaukaka Yesu zuwa mafificiyar matsayi?—Filibbiyawa 2:9.