Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Yaya Kamanin Yesu Yake?

Yaya Kamanin Yesu Yake?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Da yake Littafi Mai Tsarki bai fadi kome game da kamanin Yesu ba, ba wanda ya san ainihin kamaninsa. Kuma wannan ya nuna cewa sanin kamaninsa bai da wani muhimmanci. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya fadi wasu abubuwa game da shi da ya dan kwatanta yadda yake.

  • Wasu abubuwa: Da yake Yesu Ba-Yahude ne, babu shakka ya gaji wasu abubuwa daga mahaifiyarsa. (Ibraniyawa 7:14) Kuma bai bambanta da wasu mutane ba. Akwai lokacin da ya bar Galili a asirce kuma ya je Urushalima ba tare da mutane sun gane shi ba. (Yohanna 7:​10, 11) Kuma Yesu da almajiransa babu wani bambanci tsakaninsu shi ya sa a lokacin da ake so a kama shi, wadanda suka zo su kama shi ba su gane shi ba sai da Yahuda ya nuna musu shi.​—⁠Matta 26:​47-49.

  • Tsayin sumansa: Yesu bai bar dogon tsuma ba domin Littafi Mai Tsarki ya ce ‘kaskanci ne ga namiji ya sāke suma.’​—⁠1 Korintiyawa 11:14.

  • Gemu: Yesu ya bar gemu. Kuma ya bi dokar Yahudawa ne cewa kada maza su riƙa ‘ƙwaƙwafa [ko kuma aske] gemunsu.’ (Levitikus 19:27; Galatiyawa 4:⁠4) Ban da haka ma, annabcin Littafi Mai Tsarki game da irin wahalar da Yesu zai sha ya ambaci gemunsa.​—⁠Ishaya 50:⁠6.

  • Jikinsa: A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ya yi tafiya kilomitoci da yawa kuma hakan ya nuna cewa yana da koshin lafiya. (Matta 9:35) Sau biyu ya kori Yahudawa masu sana’a a haikali kuma ya tutture teburan kudade da suke canjawa kuma ya kori tumakinsu da bulala. (Luka 19:​45, 46; Yohanna 2:​14, 15) Littafin nan McClintock and Strong’s Cyclopedia ya ce: “Dukan labaran hidimar Yesu sun nuna cewa yana da koshin lafiya sosai.”​—⁠Kundi na IV, shafi na 884.

  • Halinsa: Yesu yana da tausayi sosai, daga ka gan shi, ka ga mai tausayi. (Matta 11:​28, 29) Mutane iri-iri sun zo wurin Yesu don ya taimaka musu kuma ya karfafa su. (Luka 5:​12, 13; 7:​37, 38) Yara ma sun so kasancewa da Yesu.​—⁠Matta 19:​13-15; Markus 9:​35-37.

Wasu karyace-karyace game da sifar Yesu

Karya: Wasu sun gaskata cewa Yesu dan Afirka ne don littafin Ru’ya ta Yohanna ya kwatanta sumansa da ulu, tafin kafarsa kuma da “gogaggen jan ƙarfe.”​—⁠Ru’ya ta Yohanna 1:​14, 15.

Gaskiya: Wasu abubuwan da aka rubuta a littafin Ru’ya ta Yohanna ba a zahiri ba ne. (Ru’ya ta Yohanna 1:⁠1) Saboda haka, yadda aka kwatanta sumansa da kafafunsa suna nuna halin Yesu ne bayan da aka ta da shi daga mutuwa ba kamaninsa a lokacin da yake duniya ba. Saboda haka, sa’ad da Ru’ya ta Yohanna 1:14 ta kwatanta sumansa “kamar farin ulu, farare fat kamar dusar ƙanƙara,” kalar ne yake kwatanci da shi ba kaurin sumar ba. Hakan ya kwatanta yadda hikimarsa take da yake ya yi shekaru da yawa. (Ru’ya ta Yohanna 3:14) Don haka, ba wai wannan ayar tana kwatanta sumar Yesu da ulu ba ne, a maimakon haka, tana kwatanta wa da snow ko dusar kankara.

Kafafun Yesu ya yi kama da na “gogaggen jan ƙarfe, sai ka ce an gyarta shi cikin tanderu.” (Ru’ya ta Yohanna 1:15) Ban da haka ma, fuskarsa “tana kama da rana sa’anda tana haskakawa da ƙarfinta.” (Ru’ya ta Yohanna 1:16) Babu wata kabila da fatarsu ta yi kama da kwatancin da ake yi a nan. Don haka, abin da aka fada a wannan wahayin a alamance ne kuma yana kwatanta Yesu da aka ta da daga mutuwa cewa yana da “mazauni cikin haske wanda ba shi kusantuwa.”​—⁠1 Timotawus 6:⁠16.

Karya: Yesu wani kumame ko bai da kuzari.

Gaskiya: Yesu mai kuzari ne sosai. Alal misali, a lokacin da taron jama’a suka zo su kama shi, ya fito baro-baro ya ce ga shi nan. (Yohanna 18:​4-8) Inda Yesu ba shi da kuzari, da ba zai iya yin aikin kafinta da ake bukatar mutum ya riƙa aiki da kuzari ba.​—⁠Markus 6:⁠3.

To me ya sa wani ya taimaka wa Yesu daukan gungumen azaba? Kuma me ya sa ya mutu kafin barayin da aka rataye su tare? (Luka 23:26; Yohanna 19:​31-33) Yesu ya sha wahala sosai kafin a kashe shi. Bai yi barci ba, tun daddare yana tunanin irin wahalar da zai sha. (Luka 22:​42-44) Yahudawa sun masa wulakanci sosai daddare, kuma da safiya ta yi, sai Romawa ma suka azabtar da shi. (Matta 26:​67, 68; Yohanna 19:​1-3) Watakila wadannan abubuwan ne suka sa ya mutu da sauri.

Karya: Yesu a kullum yana bakin ciki.

Gaskiya: A lokacin da Yesu yake duniya, duk abubuwan da ya yi sun nuna halin Ubansa Jehobah da Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah mai-albarka” ko farin ciki ne. (1 Timotawus 1:11; Yohanna 14:⁠9) Kuma Yesu ya koya ma wasu yadda za su kasance da farin ciki. (Matta 5:​3-9; Luka 11:28) Wadannan abubuwan sun nuna cewa Yesu a kullum yana fara’a.