Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Idan Mace da Namiji Suna Soyayya, Daidai ne Su Yi Zama Tare Babu Aure?

Idan Mace da Namiji Suna Soyayya, Daidai ne Su Yi Zama Tare Babu Aure?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki ya ce “fasikai . . . Allah za shi shar’anta.” (Ibraniyawa 13:4) Kalmar Helenanci na ‘fasikanci’ por·nei′a, ya haɗa da jima’i kafin aure. Saboda haka, ba daidai ba ne wajen Allah waɗanda suke soyayya marasa aure su yi zama tare—ko idan suna shirin za su yi auren nan gaba.

Idan suna son juna sosai kuma fa? Har ila, Allah yana bukatar su yi aure kafin su yi jima’i. Allah ne ya halicce mu don mu ƙaunaci juna. Ainihi shi Allah ƙauna ne. (1 Yohanna 4:8) Saboda haka, yana da dalili mai kyau da ya ce jima’i domin ma’aurata ne kaɗai.